Labarin mahaifi da dansa masu kwanciya da diyarsa

Labarin mahaifi da dansa masu kwanciya da diyarsa

- An gurfanar da wani magidanci da dashi bisa zargin lalata da yarinya yar shekara 9

- Lamarin ya baqantawa mutane rai, a kafafen sada zumunta

- Kotu tayi zimmar hukunci

Labarin mahaifi da dansa masu kwanciya da diyarsa
Labarin mahaifi da dansa masu kwanciya da diyarsa
Asali: UGC

Wannan mutun dan kimanin shekaru 65, da danshi dan shekaru 19 dai an gurfanar dasu a gaban kotu bisa zargin lalata da yarinya yar shekaru 9 kacal. Wadannan mutane wato Lawal Angala da danshi Isa dai sun gurfanar a gaban kotun majistire dake katsina, bisa zargin laifin fyade Wanda ya sabawa sashi na 283 na kundin penal code.

Mahaifiyar ita wannan yarinya ce dai ta shigar da kara gaban yansanda wadanda suka kame wadannan mutane tare da mika su ga kuliya manta sabo. Kotun dai ta tabbatar da cewa har yanzu dai bincike yana gudana game da wannan al'amarin tare da dage sauraren karar zuwa January 24, 2019.

DUBA WANNAN: Kudin da Lakcarori ke nema, N1Tr, kafin su daina yajin aiki, shi ake kashewa duk shekara, a kasashen waje don neman ilimin - Bincike

A wani bangare daban kuma yan sanda sun cafke wani me sana'ar achaba bisa zargin lalata da yarinya yar shekara 14 a garin legas, kwamishinan yan sandan garin ne dai ya tabbatar da faruwar wannan al'amarin ga manema labarai saidai rahotanni sun bayyana cewa itafa wannan yarinyar yar shekara 14 kacal fa ba dan acabar ne ya fara lalatar ba, harda mahaifinta da kuma wani maigadi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng