Harin Boko Haram: An tabbatar da mutuwar Kaftin Kabiru Hamza

Harin Boko Haram: An tabbatar da mutuwar Kaftin Kabiru Hamza

A yau, Laraba, ne aka samu tabbacin labarin rasuwar hazikin kwamandan rundunar soji, Kaftin Kabiru Hamza, sakamakon harin kwanton bauna da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai kwanakin baya a jihar Borno.

Kafin rasuwar sa, Kaftin Hamza ya kasance shugaban rundunar soji da aka jibge a sansanin sojoji na garin Metele.

Rahoton da Premium Times ta wallafa ya bayyana cewa a kalla sojoji 113 na 157 bataliya suka rasa ransu sakamakonn harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a ranar 18 ga watan Nuwamba a sansanin soji da ke Metele.

An kuma tabbatar cewa har yanzu akwai wasu sojoji 153 da ba a gano inda suke ba kimanin mako guda bayan harin da aka kai a sansanin na sojin kamar yadda wasu manyan shugabanin soji suka fadi.

Harin Boko Haram: An tabbatar da mutuwar Kaftin Kabiru Hamza
Kaftin Kabiru Hamza
Asali: Facebook

Wadanda aka kashe sun hada da kwamandan bataliyan wanda majiyar Legit.ng ta bayyanawa cewa soja ne mai mukamin laftant kanal.

DUBA WANNAN: Harin Metele: Yadda na tsira da raina - Sojan Najeriya

An kuma gano cewa mataimakin kwamandan bataliyan da jami'in leke asiri da kuma wasu manyan jami'an soji biyu suna daga cikin wadanda aka kashe a harin da Boko Haram ta kai misalin karfe 6 na yammacin Lahadi da ta gabata.

A ranar 20 ga watan Nuwamba da Premium Times ta fara wallafa labarin harin, hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewa kwamandan battaliyan ne kawai ya rasu da wasu sojoji 12.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel