Na dauki dawainiyar 'yan siyasa da dama a baya - Atiku

Na dauki dawainiyar 'yan siyasa da dama a baya - Atiku

- Na bata kudi da yawa dan ganin an samu mace a matsayin mataimakiyar gwamna

- Ya shawarci 'yan siyasa dasu dinga zabar mace a matsayin mataimakiyar su

- Tun shekara ta 1999 yake kokari wajen yaga an samu mace a matsayin mataimakiya amma har yanzu ba nasara

Na dauki dawainiyar 'yan siyasa da dama a baya - Atiku
Na dauki dawainiyar 'yan siyasa da dama a baya - Atiku
Asali: Depositphotos

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya bata kudade da dama wajen ganin an samu mace a matsayin mataimakiyar gwamna a jihohin arewa.

Tsohon mataimakin Shugaban kasar Atiku Abubakar ya shawarci yan siyasa dasuyi kokari wajen sanya mace a matsayin mataimakiyar su.

Yace tun shekara ta 1999 yake kokari akan hakan amma har yanzu bai samu nasara ba.

"Na dauki nauyin mata don su zama mataimakan gwamnoni inda kudi na da dama suka tafi akan hakan amma har zuwa yanzu ban samu nasara ba".

DUBA WANNAN: EFCC ta bayyana yadda aka tafka cuwa-cuwar Diesel a gaban kotu

Ya bayyana cewa zaiyi iyakar kokarin sa dan ya nuna masa godiyar sa a garesu wanda mahaifiyar sa sanadi.

"Maganar gaskiya idan har kana bukatar fidda mutane daga talauci to ka samawa mata aikin yi cikin gaggawa zaka iyalai sun fita daga cikin talauci, a halin yanzu Najeriya tana daga cikin jerin kasashen dake fama da talauci,saboda haka muna bukatar bunkasa matanmu dan ganin mun fita daga wannan halin".

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng