EFCC ta bayyana yadda aka tafka cuwa-cuwar Diesel a gaban kotu

EFCC ta bayyana yadda aka tafka cuwa-cuwar Diesel a gaban kotu

- Asirin yanda aka sace mai diesel ya tonu

- Hadin baki ne tsakanin Masana'antar kasar waje da wasu guda biyar

- Man diesel din ya kai na dala miliyan takwas da rabi, watau $8.4m

EFCC ta bayyana yadda aka tafka cuwa-cuwar Diesel a gaban kotu
EFCC ta bayyana yadda aka tafka cuwa-cuwar Diesel a gaban kotu
Asali: Depositphotos

Emefun Etudo, lauyan mai kara ya bayyana a gaban kotun laifuka na musamman dake Ikeja inda ya bayyana hadin bakin sace man diesel na dala miliyan 8.4 wanda masana'antar kasar waje da wasu masana'antu biyar suka yi.

Kamfanin Trafigura Beheer BVN, Trafigura PTE da abokan hadakar su na Najeriya - Mettle Energy and Gas, Rembrandt Ltd. Da Jil Engineering and oil services Ltd- na fuskantar zargin laifuka uku da suka hada da hada kai gurin aikata laifi, sata da karbar kayan sata.

Mista Etudo, shaidar EFCC ya bayyana hakan ne bayan kara karantar Bode Olanipekun, lauyan dake kare Trafigura Beheer BVN, Trafigura PTE Ltd.

Yace CPA ta bayyana zargin damfarar da yan kasuwar mai biyu sukayi, Osahon Asemota da Yusuf Kwande wadanda sune abokan hadakar kamfanin man kasar wajen.

A yayin amsa tambayoyi daga Mista Olanipekun, lauyan mai kara ya bayyana yanda Asemota da Kwande suka waskar da ton dubu goma na man diesel mallakin Nadabo Energy Limited don amfanin su.

"Ya bayyana garemu cewa inda aka load man Apapa ne a Legas ba kwatano ba kamar yanda suka sa muka yarda. Takardar ta bayyana kwangilar mai lamba 179041 tsakanin Trafigura da Rembrandt ta bogi ce, yaudara ce kuma ba kwangila bace kamar yanda suka sa Nadabo Energy suka yarda."

Mista Etudo yace Mista Kwande, daya daga cikin wadanda ake kara sun bayyana yanda aka sace cargo mai dauke da AGO a 2009 daga gurin su shi da dayan da ake kara.

DUBA WANNAN: Kududdufi ya hadiye Yaro a Kano

Kamar yadda Rotimi Jacobs, shugaban lauyoyin EFCC, yace wadanda ake zargi sunyi laifin sata daga watan Octoba 22,2008 zuwa 15 ga Disamba 2008. Yace man diesel din ya kai na da miliyan 8.4 mallakin Nadabo Energy sannan yana ajiye karkashin Springs bank daka Victoria Island.

Mai shari'a Mojisola Dada ya dage sauraron karar zuwa 13 ga watan Disamba, bayan sauraron shaidar Etudo.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng