Kududdufi ya hadiye yaro a Kano garin wanka
- Wani yaro dan shekara 13 ya fada kududdufi
- An tsinci gawar sa a ranar Laraba da safe
- An shawarci iyaye dasu sanya ido akan yayansu da kuma hanasu rabar inda ruwa yake

Asali: Twitter
Wani yaro dan shekara 13 mai suna Dayyabu Salisu ya fada a kududdufi a lokacin da yake tsaka da wanka.
Abun ya faru ne a Mariri dake kauyen Yankatsari karamar hukumar Dawakin kudu dake jihar Kano.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano Sa'idu Muhammed ya bayyanawa manema labarai afkuwar hakan a ranar Laraba.
Mr Muhammed ya bayyana cewa lamarin ya afku ne a ranar Laraba da safe inda yaron yaje wanka a kuddufin.
DUBA WANNAN: An zargi PDP da kokarin kawo fadan kabilanci a 2019
"Mun samu labarin da misalin 10.43am daga bakin Saminu Sani inda muka gaggauta aika ma'aikatan mu da misalin 10:55am".
"An samu gawar Salisu inda daga baya aka mikashi ga mahaifin sa Salisu Abdullahi".
Daga karshe ya shawarci iyaye da su rinka kula da yaran su sannan su hanasu zuwa wajen ruwa.
Kowa dai yasan matsalar wasan yara a wuraren da ruwa ya taru, inda sukan je wanka, su kwaso cutuka, su kuma dauko datti, maimakon wanke shi, bayan ga wuraren wanka nan a otal-otal, da bai ffi a kashe N500 ba. Ko matsalar ta waye wa ce?
Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.
Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng