Kada ka farfado mana da fadan kabilanci a jihar mu - dan takarar APC ya gargadi na PDP a Legas

Kada ka farfado mana da fadan kabilanci a jihar mu - dan takarar APC ya gargadi na PDP a Legas

- Jimi Agbaje, Dan takarar jam'iyyar PDP ya tada kura a shafin shi na tweeter

- Ya maida martani ne ga Sanwo-Olu Dan takarar jam'iyyar APC akan tattaunawar da aka yi dashi a talabijin

- Agbaje ya zargi Sanwo-Olu da zama yaron wani Dan siyasa da kasa samar da cigaba a jihar Legas a cikin shekaru 20

Kada ka farfado mana da fadan kabilanci a jihar mu - dan takarar APC ya gargadi na PDP a Legas
Kada ka farfado mana da fadan kabilanci a jihar mu - dan takarar APC ya gargadi na PDP a Legas
Asali: UGC

Jimi Agbaje, dan takarar jam'iyyar PDP ya tada kura a shafin shi na twitter.

Da yammacin ranar talata, 11 ga watan Disamba 2018,Agbaje ya maida martani ga Sanwo-Olu Dan takarar jam'iyyar APC akan tattaunawar da aka yi dashi a talabijin.

Agbaje ya zargi Sanwo-Olu da zama yaron wani Dan siyasa da ya kasa samar da cigaba a jihar Legas a cikin shekaru 20.

A lokacin da ya maida martanin ga Sanwo-Olu akan cewa da yayi Legas bata son inyamurai daga yankin kudu maso gabas. Agbaje ya rubuta cewa "Masu zabe basu manta da barazanar da wani basaraken yarbawa yayi wa inyamurai ba da suke goyon bayan APC"

Ya rubuta a shafin tweeter dinshi, "Akan Legas da inyamurai: Ba gaskiya bane ace Legas basa son inyamurai. Eh, Legas basa son inyamurai, taka siyasar ai nayi. Furucin basaraken nan na 2015 na nan daram a zukatan masu zabe. Yanzu yana aiki da fadar shugaban kasa. Kila abubuwa sunyi ma yawa ko ka manta baka tunawa dashi a yanzu."

DUBA WANNAN: Jima'i a mota bai saba doka ba - Police

'Furucin basarake' da Agbaje ke nufi shine na Oba din Legas, Rilwan Akiolu, a 2015 yayi barazana ga inyamurai dasu zabi Akinwumi Ambode na jam'iyyar APC. Basaraken yace in har inyamurai basu zabi Dan takarar APC ba to zasu bace a Legas inda Ambode din ya kada Agbaje.

Da safiya laraba ne Sanwo-Olu yayi rubutu a shafin shi na tweeter don taka ma abokin adawar shi birki.

Ya ja kunnen shi da cewa yakin neman zaben ayi shi ne da hujjoji ba wai da cusa rikicin kabila ba a jihar Legas.

"Wannan zaben zai zamo ne na wanda ke da kudurori mafi inganci don jagorantar jihar Legas. Ba wai na zagi da karyace karyace ba. Banda kuma saka rikicin kabila a tsakanin yan jihar."

Sanwo-Olu ya hori Agbaje da ya kokarta wajen tallata kanshi ga jama'ar jihar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng