2019: Sarkin Kano ya kirayi Mata kan zaben 'yan takara ma su akida ta kare hakkin su

2019: Sarkin Kano ya kirayi Mata kan zaben 'yan takara ma su akida ta kare hakkin su

- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu, ya kirayi Mata kan zaben shugabanni na gari ma su akida ta kare hakkokin su

- Sarki Sanusi ya karbai bakuncin wata kungiyar Mata a fadarsa da ke tantagwaryar birni na Kanon Dabo

- Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya nemi Mata da su tashi tsaye wajen fidda jagorori ma su akida ta inganta rayuwar su

A yau Talata, 12 ga watan Dasumba na 2018, Mai martaba Sarkin Kano kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Mallam Muhammadu Sanusi na biyu, ya yi kira tare da kalubalantar Mata dangane da zaben kasa na 2019.

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, ya kirayi Mata tare da shawartar su akan jefa kuri'un su ga 'yan takara ma su akida da kudurori na kare hakkoki gami da inganta rayuwar su a cikin al'umma.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Sarkin na Kanon Dabo, ya kalubalanci Mata a Najeriya da su zabi shuwagabanni ma su akida da mufofi na yakar duk wani cin zarafi da keta haddin ma su haddi da tasirin hakan zai kawo inganci na ci gaba a rayuwar su.

2019: Sarkin Kano ya kirayi Mata kan zaben 'yan takara ma su akida ta kare hakkin su
2019: Sarkin Kano ya kirayi Mata kan zaben 'yan takara ma su akida ta kare hakkin su
Asali: Depositphotos

Sarki Muhammadu Sanusi na biyu, ya yi wannan kira ne cikin fadarsa da ke tantagwaryar Birnin Kano, yayin karbar bakuncin wata kungiya mai karfin gaske da ta kaddamar da taron ta na Mata zalla da mai lakabin "ababen da suka shafi Mata" ta MATA 2018.

A yayin da yake haskaka takaicin sa dangane da yadda ba bu wani dan takara da ya daura damarar yakin neman zaben sa tare da Mata cikin dukkanin 'yan takarkaru na zaben 2019, Sarki Sanusi ya bayyana cewa dole Mata su mike tsayu domin kwato 'yancin su a kasar nan.

KARANTA KUMA: Mu hada kai domin yakar cin hanci da rashawa - Peter Obi

Sarki Sanusi ya gargadi Mata kan juya bayan su tare da yakar duk wani dan takara da ba zai kare hakkokin su ba tare da yi ma su wakilci na gari. Ya kuma yabawa kungiyar dangane da wannan hobbasa da zai kasance abin koyi ga Matasan Mata.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, an yi jimami yayin binne Mai Martaba Sarkin Kasar Fantswan na Kafanchan, da ya riga mu gidan gaskiya tun a ranar 6 ga watan Dasumba bayan wata 'yar takaitacciyar rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng