Yawan arzikin Pastors na Najeriya a bana, inji jaridar duniya ta Forbes
- Wasu daga cikin manyan malam coci sun tara manyan kudade
- Ko meyasa ba'a bayyana partor din dayafi kowanne kudi a duniya
- Amma kuma ana bayyana wanda yafi kowa talauci a kasar

Asali: Facebook
Wani abun mamaki wasu daga cikin manyan malaman coci sun mallaki makudan kudade wanda mafi karanci daga cikin su sune wanda yake da dala miliyan $10m.
A kasar nan ana bayyana mutanen da suka fi kowa kudi amma ba'a bayyana malamin coci ko masallatai da suka tara arziki harda jirage daga arzikin da suke amsa daga hannun talakawa.

Asali: UGC
Ko ya kamata a dinga kama wadanda suka yi wa gwamnati zamba, ko wadanda ke yi wa jama'a zamba ta hanyar kudade kamar su Swiss Golden da MMM, amma ba'a batun malamai dake yaudarar talaka su amshe musu kudi?
Ma iya tambaya, ta yaya ma suka mallaki wadannan kudade?
Misali, jaridar Forbes ta bayyana a 2018, manyan malaman addini a NAjeriya da dukiyar dda ake hasashe sun tara:
- TB Joshua ya mallaki $10.
- Enoch Adeboye ya mallaki $39m
- Chris Oyakhilome na Christ Embassy, ya mallaki $50m
- David Oyedepo ya mallaki $150m harda jirgin kansa na yawo..

Asali: Depositphotos
Akwai haraji dai da coci ke karba daga mabiya na kashi 10/100 kan duk wata dukiya da mutum ya sha wahala ya tara, inda wasu Pastor ma kance wai in mutum bai biya ba babu shi babu aljanna.

Asali: UGC
An kuma sha jin cewa, limaman cocina a Najeriya sun fi na kowacce kasa kudi a duniya, inda suka maida wa'azi kamar neman kudi.
Wasunsu suna ma da jiragen su na yawo, bayan kuwa kasar NAjeriya ta tara talakawa miliyoyi da bassu da tabbacin cin yau balle na gobe.
DUBA WANNAN: Ina aka kwana kan batun kirkirar jihohi?
A dai duniya, an sha jin irin yadda wadannnan Pastor ke iya warkar da cutuka da bada karama, da ma iya fadin abubuwan da zasu faru a badi, sai dai ba'a ganin agajinsu a asibitoci, ba kuma a ganinsu suna ziyartar asibiti don warkas da jama'a.
Ba'a kuma taba ganin Pastor ya aika karffin ikon da suke kuri da shi na mu'ujiza taje Sambisa yakin 'yan ta'adda ba, duk da sukan yi ikirarin su lallai suna aiki tare daa mala'iku masu karfi.
Ko yaushe talakan Najeriya zai gane makaranta da ilimin boko ke kawo qere-qere da ci gaba, ba a tafi da yara a bautar dasu wuraren ibadu ba? Wannan kalubale ne a kan kowacce al'umma.
Sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng