Siyasar 2019 a Yobe ta dauki dumi - Ali Zanna, na ukku a jihar yayi murabus

Siyasar 2019 a Yobe ta dauki dumi - Ali Zanna, na ukku a jihar yayi murabus

- Kakakin majalisa a jihar Yobe yayi murabus

- Yabar kujerar tasa ne bayan ya share shekara bakwai da rabi a kai

- Majilisar ta amince da ajjiye aikin nasa inda nan take ta nada wani

Siyasar 2019 a Yobe ta dauki dumi - Ali Zanna, na ukku a jihar yayi murabus
Siyasar 2019 a Yobe ta dauki dumi - Ali Zanna, na ukku a jihar yayi murabus
Asali: Depositphotos

Jigo a siyasar jihar Yobe, kuma na ukku a jihar, kakaki daga jam'iyya mai mulki, APC, a majalisar jihar Yobe Rt. Hon Dala Dogo ya ajjiye mukamin sa.

Hon. Dogo ya ajjiye mukamin nasa ne bayan ya share shekara bakwai da rabi akan kujerar.

Majalisar batayi kasa a gwiwa ba ta karbi wannan batu nashi inda a take ta nada wani a madadin shi.

Majalisar ta nada Hon.Ali Zanna don ya maye gurbin Hon. Dogo inda yayi rantsuwa a gaban sauran yan majalisa cewa zaici gaba da aiki tukuru don ganin cigaba jihar.

DUBA WANNAN: Yawan arzikin Pastors a kasar nan

Ali Zanna dai ya kasance mamba na Machina Constituency.

An rantsar dashi ne a matsayin speaker na majalisar jihar a wata cibiyar majalisar inda daukacin mambobin majalisar suka samu halartar wajen.

Ana kan sauyin sheka har yanzu tsakanin 'yan siyasa, musamman yanzu da saura kwanaki kadan ayi zaben 2019.

Tun dai bayan da Adams Oshiomhole ya karbi iko da jam'iyyar APC, ake ta kara samun matsalolin cikin gida, inda a wasu jihohin ma ake samun matsalar barazanar anti-party, musamman a matakin zabukan gwamnonki.

Wannan ya kai yanzu babu 'yan takarar APC ma kwata-kata a wasu jihohin.

Sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng