‘Na Gina Masallatai’: Gwamna Ya Karyata Cewa Bai Son Musulunci a Jiharsa

‘Na Gina Masallatai’: Gwamna Ya Karyata Cewa Bai Son Musulunci a Jiharsa

  • Gwamnatin Oyo ta yi watsi da zargin kungiyar MURIC cewa Gwamna Seyi Makinde na kyamar Musulunci
  • Gwamnatin ta bayyana cewa Makinde ya gina masallacin Omituntun tun kafin ya zama gwamna, tare da daukar limami
  • Ta kuma ce gwamnan ya cika alkawarin sake gina masallacin Adogba da aka rushe yayin aikin hanyar Iwo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Gwamnatin jihar Oyo ta yi watsi da zargin kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) cewa Gwamna Seyi Makinde na kyamar addinin Musulunci,.

Gwamnatin ta tabbatar da cewa ayyukan gwamnan sun nuna akasin hakan kuma ba shi da wani kulli ga Musulmai.

Gwamna ya kare kansa kan kin jinin Musulmi
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo. Hoto: Seyi Makinde.
Source: Facebook

Gwamnatin ta bayyana cewa ayyukan da Makinde ya gudanar tun kafin ya shiga siyasa da kuma lokacin mulkinsa sun nuna goyon bayansa ga Musulmi da harkokin addinin Musulunci, cewar Punch.

Kara karanta wannan

"Nan ba da daɗewa ba yan Najeriya za su fara murna da tsare tsaren Shugaba Tinubu"

Mai ba gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Dakta Sulaimon Olanrewaju, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamban 2026.

Olanrewaju ya ce zargin MURIC bai da tushe, yana mai cewa ayyukan mutum sun fi kalamansa bayyana hakikanin matsayinsa.

Gwamnatin Oyo ta lissafa ayyukan Makinde ga Musulmi

A cewar sanarwar, mutumin da ke kyamar Musulunci ba zai kashe kudinsa wajen gina masallaci ba, ya dauki limami aiki, ya tallafa wa shirye-shiryen addinin Musulunci da kungiyoyin Musulmi.

Ya kara da cewa irin wannan mutum ba zai rika gudanar da bukukuwan sabuwar shekarar Musulunci ta hanyar ayyana ranar hutu ga ma'aikata ba.

Gwamnatin ta bayyana cewa tun kafin Makinde ya zama gwamna, ya gina masallacin Omituntun tare da daukar limami da zai rika jagorantar sallar jama'a.

Ta ce iyalan Omituntun sun shafe shekaru suna hulda da al'ummar Musulmi ta hanyar shirya wa'azin watan Ramadan da sauran shirye-shiryen addini.

Kara karanta wannan

Matasa sun hargitsa wajen da Shettima ya je kamfe din APC na 2027

Sanarwar ta tambayi dalilin da zai sa mutumin da ake zargi da kyamar Musulunci ya kashe kudinsa wajen gina masallaci tun kafin ya samu mukamin gwamnati.

Ana zargin gwamna da kin Musulmi
Taswirar jihar Oyo da aka zargi gwamnan da kin Musulunci. Hoto: Legit.
Source: Original

Gwamnati ta kalubalanci masu sukar gwamnan

Olanrewaju ya kalubalanci masu sukar Makinde da su bayyana ko wane ibadar Musulunci gwamnatinsa ta haramta tun bayan hawansa mulki a shekarar 2019.

Ya kuma bukaci su bayyana ko akwai wata cibiyar Musulunci da aka rushe, ko wani hakki da aka kwace daga hannun Musulmi a karkashin gwamnatin.

A cewarsa, babu wata ibada da aka haramta ko wata cibiya ta Musulunci da aka dakatar a jihar, cewar Tribune.

Ya ce a maimakon haka, gwamnatin Makinde ta amince da muhimmancin kalandar Musulunci ta hanyar ayyana ranar hutu domin tunawa da Hijira, wato sabuwar shekarar Musulunci.

Makinde ya sake gina masallacin Adogba

Gwamnatin ta kuma yi magana kan rushe masallacin Adogba Central Mosque a lokacin aikin sake gina mahadar Iwo Road.

Ta ce masu sukar gwamnan ba sa bayyana yadda ya ziyarci masallacin kafin rushe shi, ya yi ibada tare da al'ummar Musulmi, ya yi musu bayanin dalilin da ya sa dole a rushe ginin saboda aikin hanya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi yadda ya yi tukin tasi domin rufa wa kansa asiri a Amurka

Olanrewaju ya ce Makinde ya kuma yi alkawarin sake gina masallacin, kuma daga bisani ya cika alkawarin tare da mika sabon masallacin mai kayayyakin zamani ga al'ummar yankin.

Gwamna zai gina wa Musulmi masallatai

An ji cewa Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya amince da sayen wani gida domin mayar da masallacin wucin gadi zuwa na dindindin.

An sayi gidan ne a yankin Go-Slow da ke Birnin Kebbi, kusa da gidan Abubakar Malami, tsohon ministan shari’a.

Matasa sun yabawa matakin, inda suka roki gwamnan ya gina masallaci da makarantar Islamiyya domin yaransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.