An bizne Sarki Agwam Fantswan na Kasar Kafanchan da ya cika kwanaki

An bizne Sarki Agwam Fantswan na Kasar Kafanchan da ya cika kwanaki

Mun samu labari cewa an birne Marigayi Mai Martaba Sarkin Kasar Fantswan na Kafanchan wanda ya cika kwanakin baya. An birne Sarkin ne a Masarautar sa sa da ke cikin Garin Zikpak a Yankin Kudancin Kaduna.

An bizne Sarki Agwam Fantswan na Kasar Kafanchan da ya cika kwanaki
Mallam Musa Didam ya bar Duniya yana shekara 85
Asali: Twitter

An yi jana’izar Mai Martaba Agwam Fantswan, Musa Didam ne a Karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna a Ranar Juma’ar nan. Sarkin ya bar Duniya ne a Ranar Alhamis 6 ga Watan Disamban nan bayan yayi fama da rashin lafiya.

Sarkin na Kafanchan yana cikin Masu rike da Masarautun Jihar Kaduna kuma yana da sanda mai ikon a 2. Manyan mutanen Yankin Jihar wanda su ka hada da Sanatan Kudancin Kaduna Danjuma Laah sun halarci wannan jana’izar.

KU KARANTA: An zabi sabon Kakakin Majalisar dokoki a Jihar Katsina

Sanata Danjuma La’ah ya bayyana cewa Sarkin yayi rayuwa abin koyi inda yace Sarkin mutumun kirki ne. Mai Martaba Musa Didam ya cika ne yana da shekaru 85 a Duniya kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar nan ta Daily Trust.

Sarkin Kagoma, Kanal Paul Wyoms mai ritaya yana cikin wadanda aka bizne Marigayi Sarkin na Kafanchan a gaban su. Mai martaba Kpop-Gwong ya yabawa Takwaran na sa, ganin yadda ya rike Kasar sa ba tare da nuna banbanci ba.

Haka-zalika, Babban Limamin Kirista na Garin Zonkwa, Rabaren Haruna Kato, na cocin ECWA, yayi huduba mai ratsa jiki a wajen bizne Mamacin inda yayi kira ga Jama’a su komawa Ubangiji kafin ajali ya dauke su babu tsammani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel