Dubu Ta Cika: DSS Ta Cafke Matashiyar da Ke Safarar Makamai a Nasarawa
- DSS ta kama Aisha Mohammed, mai shekara 23, a Keffi da harsasai 202 da kuma gidan jigidar bindiga guda uku babu harsasai a ciki
- Hukumar ta kuma kama wasu mutum huɗu a wasu samame, inda ta kwato harsasai sama da 2,000 masu nau'o'i daban-daban
- Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yaba wa jami'an tsaro tare da alƙawarin ci gaba da tallafa musu wajen yaƙi da laifuffuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Nasarawa - Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (DSS) ta kama wata mata mai shekara 23 da wasu mutum huɗu da ake zargi da safarar makamai, a wasu samame daban-daban da ta gudanar a Jihar Nasarawa.
A yayin samamen, jami'an hukumar sun kwato harsasai sama da 2,000, ciki har da na bindigogi masu nau'o'i daban-daban.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce wata mata mai suna Aisha Mohammed, mazauniyar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, na cikin waɗanda aka kama.

Kara karanta wannan
Bayan kama su da laifi, za a rataye jami'an tsaro 4 har lahira a Arewacin Najeriya
An kama Aisha ne a Keffi, inda aka same ta da harsasai 202 masu girman 7.62mm da kuma magazin bindiga guda uku babu harsasai a ciki.
An kama wasu mutum 4 a wasu samame
Sauran waɗanda aka kama tsakanin watan Agusta da Satumban 2026 sun haɗa da Hassan Sani, mai shekara 40; Abdulkadir Idrissa, mai shekara 41; da Salihu Garba, mai shekara 70, wanda aka fi sani da Nabayi.
Rahotanni sun nuna cewa jami'an DSS sun kwato harsasai 678 masu girman 7.62mm da kuma wasu harsasai 99 masu girman 7.5mm daga hannun waɗannan mutum uku, tare da wasu kayayyaki.
Haka kuma, a wani samame daban da aka gudanar a watan Agusta, jami'an hukumar sun kama wani mutum da ake zargi da safarar makamai mai suna Ismail Lawalli.
Lawalli, ɗan asalin Jihar Zamfara, an kama shi ne a kan hanyar Keffi zuwa Abuja, inda jami'an suka kwato harsasai 1,262 na nau'o'i daban-daban daga hannunsa.

Kara karanta wannan
Nesa ta zo kusa: CDCFIB za ta sake bude shafin ɗaukar ma'aikata a hukumomi 4 a Najeriya
Gwamnan Nasarawa ya yaba wa DSS
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yaba wa jami'an DSS bisa samamen da suka gudanar da kuma kwato makaman da ake zargin ana safarar su, cewar rahoton jaridar The Punch.
Gwamnan ya bayyana nasarar samamen a matsayin wani muhimmin ci gaba a ƙoƙarin da ake yi na dakile safarar makamai a jihar.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaransa, Ibrahim Addra, ya fitar, Sule ya yabawa DSS da sauran hukumomin tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi na yaƙi da aikata laifuffuka.
Ya kuma amince da muhimmancin haɗin gwiwar da ke tsakanin hukumomin tsaro da gwamnatinsa, tare da alƙawarin ci gaba da ba su goyon baya domin gudanar da ayyukansu.
An buƙaci jama'a su taimaka kan tsaro
Gwamna Sule ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan yaƙi da aikata laifuffuka da kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Ya kuma yi kira ga al'umma da su ba hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar taimaka musu da bayanan da za su taimaka wajen gano masu aikata laifuffuka da kuma tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.

Source: Facebook
Mutanen gari sun kashe 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa mazauna garin Birnin Tudu da ke karamar hukumar Gummi a Jihar Zamfara sun ce sun kashe ’yan bindiga sama da 30.
Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun zo da ɗaruruwan babura, suka kewaye ƙauyen sannan suka fara harbe-harbe.
Asali: Legit.ng
