Kishi kumallon mata: Uwargida ta kashe kanta da yayanta biyu saboda Magida zai ƙaro amarya

Kishi kumallon mata: Uwargida ta kashe kanta da yayanta biyu saboda Magida zai ƙaro amarya

Ke duniya ina zaki damu ne, har yanzu kuma da alama har gobe dadaddiyar dabi’ar nan ta mata watau kishi ba zai taba rabuwa dasu ba, tunda dai ta tabbata har a zamanin iyaye da kakanni ma an yi kishi da juna, sai dai kishi na irin wannan zamani na neman ya wuce gona da iri.

Anan mun samu rahoto wata Mata yar kasar Kenya mai suna Ruka Wasuna mai shekaru 26 da ta halaka kanta, sa’annan kafin nan ta halaka yayanta data haifa guda biyu kawai don mijinta ya kamma shirin dauko mata abokiyar zama, watau amarya, ko ace kishiya.

KU KARANTA: Iyalan tsofaffin ma’aikatan NITEL su 500 da suka mutu sun samu N1,500,000,000 daga Buhari

Kishi kumallon mata: Uwargida ta kashe kanta da yayanta biyu saboda Magida zai ƙaro amarya
Gobara
Asali: Depositphotos

Legit.com ta ruwaito matar nan ta kashe kanta da yaran nata ne ta hanyar banka ma gidansu wuta dake unguwar Otongole a yankin Kisumu, wanda ya konasu kurmus, ba don komai ba sai don bacin ran data shiga a sakamakon kishin daya turnuketa saboda mijinta uban yayanta zai kara aure.

Mai unguwan Otongole, Simon Osege Orwa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace sun kaddamar da bincike a matakinsu, sa’annan ya kara da cewa matar ta dauki wannan mummunan mataki ne saboda rashin jituwa da ta samu da mijinta.

Mai unguwa Osege ya bayyana cewa mijin matar na shirin kara aure ne ba tare da sanin matarsa Rukia ba, amma ranar da ta samu labarin, sai ta garzaya wani gidan mai dake makwabtaka dasu, ta sayo fetir galan daya wanda tayi amfani dashi wajen banka ma gidansu wuta.

Daga karshe Mai Unguwa Osege ya bayyana cewa mijin matar na bakin aikinsa a kamfanin Eldoret ne a lokacin daya samu labarin abinda ya faru, amma tuni Yansanda sun isa idan lamarin ya faru suka kwashe gawarwakin mamatan.

Ku biyo mu a cKu biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng