Da Gwamnatin Ganduje da akidun sa nake adawa ba da shi ba – Abba Yusuf

Da Gwamnatin Ganduje da akidun sa nake adawa ba da shi ba – Abba Yusuf

‘Dan takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar PDP mai adawa yayi hira da Jaridar Daily Trust inda ya bayyana abin da ya sa yake kokarin karbe mulki daga hannun Gwamna mai-ci Abdullahi Umar Ganduje.

Da Gwamnatin Ganduje da akidun sa nake adawa ba da shi ba – Abba Yusuf
Abba Yusuf yace ba ya tsoron karo da Ganduje a 2019
Asali: Facebook

Abba Kabiru Yusuf ya bayyyana cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga layin Kwankwasiyya da yayi sanadiyyar darewar sa kan mulki a 2015. Abba Yusuf yace shi yasa yake neman kujerar Gwamna a zaben 2019.

Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda ya rike mukamai da dama a Gwamnatin Jihar Kano ya koka da yadda Gwamnatin Dr. Abdullahi Ganduje tayi watsi da ayyukan da Kwankwaso ya faro a bangaren ilmi da kiwon lafiya da aikin gona.

KU KARANTA: 2019: Atiku ne zai yi maganin yunwa a Najeriya – Inji Kwankwaso

Abba Yusuf yace idan ya samu mulkin Jihar Kano zai karasa ayyukan da Kwankwaso ya bari wanda daga ciki akwai hanyoyi da manyan gadoji a cikin Garin Kano. Yusuf yace akwai makarantun da aka soma da aka yi watsi da su.

Injiniyan ya kuma sha alwashin cigaba da rabawa ‘Yan Makaranata abinci da kayan makaranta kyauta domin bunkasa harkar ilmi da zarar ya samu mulki. ‘Dan takarar ya kuma yi alkawarin inganta harkar kiwon lafiya a fadin Jihar Kano.

KU KARANTA: Bai kamata a sake zaben shugaba Buhari ba - Inji Dattawan Arewa

‘Dan takarar Gwamnan ya bayyana cewa farin jinin Shugaba Buhari ya ragu kwarai a Kano saboda halin da jama’a su ke ciki na yunwa da wahala. A wani bangaren kuma yace Jama’a sun yi na’am da irin tafiyar Alhaji Atiku Abubakar.

Yusuf ya nuna cewa yana sa rai cewa zai tika sauran ‘Yan takarar Gwamnan Kano da kasa a zaben 2019. Yusuf ya kuma bayyana cewa ikon Allah ne ya sa aka tsaida sa takara a PDP kuma yana cigaba da hada-kai da sauran ‘Yan Kwankwasiyya.

Abba K. Yusuf yake Ma'aikatan Gwamnati da Talakawa su na kuka da Ganduje inda ya kuma ce ba ya gudun karawa da shi domin kuwa Ubangiji ne yake bada mulki. ‘Dan takarar yayi kira ga jama’a su zabi PDP a 2019 kuma su tabbatar an yi adalci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel