Manyan arewa sun halarci jana'izar Sanata Aruwa, hotuna

Manyan arewa sun halarci jana'izar Sanata Aruwa, hotuna

Da ranar yau, Lahadi, ne aka yi jana'izar marigayi Sanata Ahmad Mukhtar Aruwa a garin Kaduna. Jana'izar ta samu halartar manyan arewa da suka hada da masu tsofi da Shugabanni masu ci, 'yan siyasa, 'yan kasuwa, malaman addini da jami'an gwamnati.

Da safiyar yau din ne jaridar Legit.ng ta sanar da ku cewar labarin da ke shigo mana yanzu-yanzu daga jihar Kaduna na nuna cewa Allah ya yiwa babban dan siyasa kuma tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Ahmed Aruwa, rasuwa.

Manyan arewa sun halarci jana'izar Sanata Aruwa, hotuna
Manyan arewa sun halarci jana'izar Sanata Aruwa
Asali: Twitter

Majiya daga iyalansa ta bayyana wa Legit.ng cewar Sanata Aruwa ya rasu ne da safiyar yau, Lahadi, kuma za'ayi janaizarsa a masallacin Sultan Bello misalin karfe na rana1.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa Shekau ya buya a gida na - Dan majalisar wakilai, Monguno

Aruwa ya kasance Walin Hadejia, ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 1999 da 2007 inda ya rike kujeran shugaban kwamitin sufurin jirgin sama, ayyuka da gidaje, harkokin 'yan sanda, aikin noma da kuma kasafin kudi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel