Yadda Ibrahim Taiwo ya taba jan kunne na game da yin juyin mulki - Babangida
Kwanan nan ne mu ka samu labarin cewa tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida yayi hira da wasu ‘Yan jaridar The Cresh inda ya tabo abubuwa da dama da su ka shafi mulkin sa da gidan Soji.

Asali: Depositphotos
Babangida wanda aka fi sani da IBB ya bada labarin yadda Marigayi Kanal Ibrahim Taiwo ya taba gargadin sa game da yunkurin yin juyin mulki. Taiwo ya taba samun IBB yana karanta wani littafi na sha’anin juyin mulki ne a wancan lokaci.
Kanal Taiwo wanda yayi Gwamna kafin a kashe sa, ya fadawa Babangida ya bi a hankali tsaf da wannan littafi da yake karantawa inda ya kuma fada masa ya maida hankali kan wani babi da yake magana game bacin rana wajen kifar da Gwamnati.
A wannan babi da Taiwo ya nemi IBB ya maida hankali a kai, an yi bayani ne game da irin azabar da ke jiran duk wanda yayi yunkurin kawar da Gwamnati amma bai yi nasara ba. A doka dai ana kashe wanda aka kafa da laifin hambarar da Shugaban kasa.
KU KARANA: Abin da yasa Shekau ya buya a gida na - 'Dan majalisar Najeriya
Da aka tambayi Babangida ko wannan gargadi da aka yi masa ya shige sa, sai ya bayyana cewa babu abin da wannan jan-kunne yayi masa illa ma kara masa kwarin gwiwa. Babangida yace yana kallon juyin mulki ne a matsayin kishin-kasa da gyara.
Janar Ibrahim Babangida ya bayyana cewa bai da hannu cikin juyin mulkin da aka yi na farko a Kasar. Amma babban Sojan ya taka rawar gani daga baya, har zuwa wajen kauda yunkurin juyin mulkin da aka yi wa Janar Murtala Muhammad a 1976.
A Ranar Sallah a shekarar 1985 ne Manjo Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya hambarar da Gwamnatin da yake ciki ta Janar Muhammadu Buhari inda ya dare kan mulki har zuwa kusan karshen Agustan 1993.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng