Yayan Atiku Abubakar na Yola, yace Buhari ne zai ci zabe

Yayan Atiku Abubakar na Yola, yace Buhari ne zai ci zabe

- Tsohon ministan ilimi, Alhaji Birma Dauda yayi hasashen sakamakon zaben 2019

- Hasashen ya nuna cewa zaben zai matukar zafi

- Amma kuma za'ayi zaben cikin lumana da kwanciyar hankali

Yayan Atiku Abubakar na Yola, yace Buhari ne zai ci zabe
Yayan Atiku Abubakar na Yola, yace Buhari ne zai ci zabe
Asali: UGC

Tsohon ministan ilimi, Alhaji Birma Dauda, yayi hasashen sakamakon zaben shugabancin kasa na 2019. Dauda yace duk da dai zaben zai yi zafi amma kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari zaiyi nasara.

Da yake daga jiha daya suka fito, kuma jam'iyya daya, Atiku yakan kira Dauda da Yaya na ne a gida.

Tsohon ministan yace duk da Atiku 'Kanin shi ne' amma yana tare da 'abokin shi' (Buhari) a 2019. Ya kuma ce za'ayi zaben cikin lumana da zaman lafiya.

DUBA WANNAN: gwamnatin-jihar-bayelsa-ta-sha-alwashin-hukunta-wadanda-suka-haddasa-tarzoma-a-zaben

Zaben ne zai zamo madubin dubawa ga sauran zabuka. Ta wannan fuskar, mutane zasu zabi Buhari ba tare da sauraron yakin neman zaben da akeyi ba. Mutane zasu zabe shi saboda Nagartar shi. Ba zasu duba rashin tabbas ba. Zaben za'ayi shi cikin lumana da zaman lafiya. Da haka na yarda cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai koma kujerar shi," inji shi.

Da aka tambaye shi ra'ayin shi akan cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai yi aiki ba,Dauda cewa yayi: "Najeriya kasa ce mai mutane miliyan 180. Kowa na da nashi ra'ayin. Don haka kowa da bangaren da yake tsammani. Idan tunanin mutum almubazzaranci ne toh gaskiya bazai ga hakan ba. Mutane da yawa suna tunanin ganin hakan kuma ba zai faru ba."

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng