Audugar Al'ada: Shin me matan arewa ke bukata daga al'umma da gwamnatoci?

Audugar Al'ada: Shin me matan arewa ke bukata daga al'umma da gwamnatoci?

- Sha'anin jinin haila ba abune daya shafi mata kadai ba muma ya shafemu

- Al'ummar Hausa-fulani suna ganin wannna abu ne da bai kamata ana yamadidi dashi ba

- Ya kamata mata su dunga samun abinda zasu tsaftace kansu a yayin jinin haila a kyauta

Audugar Al'ada: Shin me matan arewa ke bukata daga al'umma da gwamnatoci?

Audugar Al'ada: Shin me matan arewa ke bukata daga al'umma da gwamnatoci?
Source: UGC

Al'ummar Hausa-fulani suna ganin bai kamata a fito cikin al'umma ana maganar jinin haila ba,ballantana har ayi muhawara akai saboda kunya irin tasu.

Amma ya zama dole muyi magana akai duba da yanda matan ke cutuwa a dalilin rashin kudin da zasu sayi abinda zasu tsaftace kansu dashi a lokacin da suke yin jinin haila.

Jinin haila ba abinda ya shafi mata kadai bane muma a matsayin mu na maza abin ya shafemu tunda abinda yayi su shi yayi mu.

Abun dubawa anan meya janyo mata suka fito suna neman a dunga basu Pad kyauta? Shin suna bukatar ta ne? Idan suna bukata shin ita pad din abar ado ce?

To wannan ba abun mamaki bane da har suka fito suna neman a dunga basu Pad kyauta,wanda da yawa daga cikin mu muna ganin hakan bai kamata ba.

Amma babban misali ko a musulunce an nunawa mata yanda zasu tsaftace kawunan su a harkar lafiya ma haka suna samun wannan ilimin amma basu da kudin da zasu sayi Pad din don su tabbatar da abinda aka koyar dasu.

DUBA WANNAN: Najeriya 2019: Abubuwa 19 da matasan Najeriya ke jira sabuwar gwamnati tayi musu, kowaye kuwa yaci zabe

A kasar nan da kuma kasashen ketare anayin allurar polio don a kubutar da kananan yara daga kamuwa da cututtuka.

Amma dan kawai wasu mata sun fito sun nemi da a dunga basu Pad kyauta an sakasu a bakin duniya ana cewa hakan ya sabawa addini da al'ada .

Shin addini ya hana mata su fita su nemi sani akan harkar jinin haila?

Daga karshe ina kira ga shuwagabannin mu na yanzu dasuyi duba akan wannan lamari su dauki matakin daya kamata na agazawa mata da Pad kyauta.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel