Hukumar NYSC ta kansile bautar kasar Davido, sai ya sake tun daga farko
- Anyi ta yamadidi da bautar kasar Davido a bana
- Yazo bautar kasa cikin mota da kaya masu tsada
- Ya fadi a Instagram cewa NYSC ta kansile nasa aikin

Asali: Instagram
Duk da yamadidi da aka yi tayi a kasar nan, kan bautar kasar masoyin waqa David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, yanzu dai mawaqin yace hukumar NYSC ta kansile bautar kasar tasa, a shafinsa na Instagram.

Asali: Instagram
A cewarsa dai, dama yazo ne yayi bautar kasar saboda ya sami damar toshe duk wata kafa da nan gaba ka iya kawo masa illa, ganin yadda 'yar takardar ta NYSC ta kori minista sukutum daga aiki a kasar nan.
Matashin wanda shekarunsa 25, ya kammala karatunsa na digiri, fannin kida a jami'ar Babcock, a 2015, amma sai yanzu ne ya gwammace yayi bautar kasar don kar ya zama ya kai 30 bayyi ba.
DUBA WANNAN: Nafi karfin maula a hannun 'yan siyasa - Oyedepo ke maida martani bayan katobaras Father Mbaka kan kin sadaqar Peter Obi ga Coci
Sa'ilin dayake taya abokinsa murnar gama tasa bautar kasar ne, wanda ya saka takardarsa a shafin Instagram, Adesegun Adeosun, yana neman a taya shi murna, sai Davido yace: "Na so dem cancel my own oo." Inda yake nufi "a haka ni kuma suka soke min nawa fah!"
Dama dai idan mutum ya fiye fashi a aikin NYSC, to za'a soke aikin nasa na shekara, kma dole ya dawo badi ya sake aikin a rabin albashi, watau N9,900. A maimakon N19,800da ake biyan kowanne kopa a wata.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng