Yadda shugaba Buhari yayi wa kabilar Ibo 'yar burum-burum

Yadda shugaba Buhari yayi wa kabilar Ibo 'yar burum-burum

- A cikin tituna da gada 69 da aka gyara a kudu maso yamma, kashi 4.48 ne kacal suke aiki lafiya lau

- Wannan rahoton da muryar jama'a ta bada ne

- Rahoton ya nuna cewa kashi biyu bisa uku na aiyukan, Gwamnatin jiha ce tayi

An gano yadda Buhari yayi wa kabilar Ibo 'yar burum-burukm

An gano yadda Buhari yayi wa kabilar Ibo 'yar burum-burukm
Source: Twitter

Kashi 4.48 na tituna da gada wanda Gwamnatin tarayya ta lissafo a cikin aiyukan ta na kudu maso gabas ne suka kammala, ake amfani dasu kuma suke lafiya, inji rahoton kungiyoyi biyu na taimakon kai da kai.

Rahoton da V2P da HOG-1 suka bada bayan duba da tantance aiyukan ya bayyana cewa kashi biyu bisa uku na kammalallun aiyukan gwamnatin jiha ce tayi.

DUBA WANNAN: Kisan jami'an tsaro a Arewa maso yamma, abin tsoro ne ko kuma tsohon lamari ne?

Aiyukan na daga cikin jerin aiyukan da ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed, ya bada a watan Augusta na 2018.

"Kashi 8.96 cikin dari na aiyukan an kammala kuma ana amfani dasu, sai dai ba a hali mai kyau ba. Sai kashi 1.49 na aiyukan an kammala su amma sun lalace."

Ana sa rai dai kabilar Igbo da yankunan Neja Delta jihohi ne da PDP tayi karfi, kuma ga dukkan alamu Atiku Abubakar zasu zaba.

Yawanci kuma daga cikinsu ne ake samun masu son kafa sabuwar kasar Bayafara.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel