Daukaka: Sarki Sanusi II zai nada mawakin Kannywood "sarkin mawakan sarkin Kano"

Daukaka: Sarki Sanusi II zai nada mawakin Kannywood "sarkin mawakan sarkin Kano"

Fadar sarkin Kano ta sanar da cewar za ta nada mawakin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Naziru Ahmad, a matsayin sarkin mawakan sarkin Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata takardar sanarwa da Munir Sanusi, shugaban ma'aikatan sarkin Kano, ya aikewa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a yau, Lahadi.

Sanarwar ta ce fadar za ta yiwa mawakin sarautar ne bisa la'akari da yabon wakokin yabo da ya ke yiwa sarki Sanusi II tun yana Dan Majen Kano.

Naziru ya rera wakoki ga sarki Sanusi II da su ka yi fice a kasar Hausa. A daya daga cikin wakokin da ya rera, Naziru ya ambaci cewar Sanusi zai zama sarkin Kano tun lokacin da ya ke rike da mukamin gwamnan babban bankin kasa (CBN).

Daukaka: Sarki Sanusi II zai nada mawakin Kannywood "sarkin mawakan sarkin Kano"
Naziru Ahmad
Asali: Twitter

Sanarwar ta umarci mawakin da ya sadu da shugaban ma'aikatan fadar sarkin Kano domin kammala shirye-shirye a kan nadin sarautar da za a yi masa.

A kwanakin baya ne rahotanni su ka yada cewar sarki Sanusi II ya nada fitaccen mawakin kudu, Korede Bello, a matsayin sarkin mawakansa bayan an ga mawakin yayin hawan sallah a Kano.

DUBA WANNAN: Yunkurin Atiku na shiga Amurka ya gamu da cikas, ya dawo Najeriya

Sai dai masarautar ta Kano ta fitar da sanarwar karyata rahoton tare da bayyana cewar mawakin aboki ne ga dan sarkin Kano.

Za a nada Naziru Ahmad a matsayin sarkin mawakan sarkin Kano ranar 27 ga watan Disamba, a fadar mai martaba sarkin Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel