Rundunar sojin sama ta yi gwajin dabarun ceton rai daga samaniya

Rundunar sojin sama ta yi gwajin dabarun ceton rai daga samaniya

A ranar 10 ga watan Satumba, 2018, rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta gudanar da wani atisaye ga dakarunta na bangaren kula da lafiya domin gwajin wasu dabarun ceton rai daga sararin samaniya.

Rundunar ta bayar da horon ne ga dakarun soji 37 da ke bangaren kula da lafiya na hukumar da aka zabo daga fadin Najeriya. An bawa dakarun horon ne a asibitin rundunar sojin sama na 261 da ke jihar Bauchi.

A sanarwar rundunar sojin, ta ce bawa dakarun soji horon zai taimaka wajen bayar da agajin gaggawa ga rundunar sojin Najeriya da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno (Ofireshon Lafiya Dole) da kuma sauran aiyukan jami'an soji fadin kasar nan.

Rundunar sojin sama ta yi gwajin dabarun ceton rai daga samaniya
Rundunar sojin sama ta yi gwajin dabarun ceton rai daga samaniya
Asali: Twitter

Rundunar sojin sama ta yi gwajin dabarun ceton rai daga samaniya
Rundunar sojin sama yayin gwajin dabarun ceton rai daga samaniya
Asali: Facebook

Rundunar sojin sama ta yi gwajin dabarun ceton rai daga samaniya
Rundunar sojin sama ta yi gwajin dabarun ceton rai daga samaniya
Asali: Twitter

Rundunar sojin sama ta yi gwajin dabarun ceton rai daga samaniya
Rundunar sojin sama ta yi gwajin dabarun ceton rai daga samaniya
Asali: Twitter

Da yake jawabi yayin kaddamar da shirin bayar da horon, shugaban sashen lafiya na rundunar sojin sama, Sale Shinkafi, wanda Kaftin Azubuike Chukwuka, darekta a sashen lafiya da hulda da jama'a ya wakilta, ya ce kwarewar dakarun sojin sama a bangaren ceton rai zai inganta aiyukan bayar da agajin gaggawa ga dakarun soji a yanayin yaki ko atisaye domin kakkabe 'yan ta'adda.

A wani labarin mai alaka da wannan da Legit.ng ta kawo ma ku, kun ji cewar gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya kaddamar tare da mika makullan motoci ga wasu jami'an soji 5 da su ka nuna bajinta a aikinsu na hidimtawa kasa.

DUBA WANNAN: Harin Metele: Hukumar soji za ta dauki matakin shari'a a kan wasu mutane

Gwamnan ya mika makullan motocin ga jami'an sojin ne yayin da ya halarci taron rundunar soji na shekarar 2018 da aka gudanar a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, shugaban rundunar soji ta kasa, ne ya jagoranci taron na wannan shekarar kamar yadda dokar taron ta tanada.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bude taron na wannan shekarar a ranar Laraba, yayin da ya kai ziyarar jaje da ta'aziyya ga dakarun soji da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno biyo bayan wani mummunan hari da mayakan kungiyar Boko Haram su ka kai kan sansanin soji da ke garin Metele, karamar hukumar Guzamala, mai makwabtaka da kasar Chadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel