Anga gwamnan Zamfara Abdul-Aziz Yari a bidiyo yana cewa akan zabe sai dai a mutu ko ayi rai

Anga gwamnan Zamfara Abdul-Aziz Yari a bidiyo yana cewa akan zabe sai dai a mutu ko ayi rai

- A cikin bidiyon dai AbdulAziz Yari ya budo wuta

- Sai yanzu shugaba Buhari ya sanya baki a lamarin

- Yace a shirye yake a kaishi kabari kan lamarin

Anga gwamnan Zamfara Abdul-Aziz Yari a bidiyo yana cewa akan zabe sai dai a mutu ko ayi rai

Anga gwamnan Zamfara Abdul-Aziz Yari a bidiyo yana cewa akan zabe sai dai a mutu ko ayi rai
Source: Facebook

A zabuka na cikin gida da aka yi a jihohi dai, ba ko'ina ne aka sami yadda ake so ba, inda sai da aka kai ruwa rana a wasu jihohin, sannan lamarin ya lafa, jihohin da gwamnoni basu ji dadin lamarin ba, sun hada da na Imo da Zamfara da jihar Ibikunle Amosun watau Ogun.

Sai kwatsam, aka gano bidiyo na gwamna Abdul-Aziz Yari na Zamfara, yana cewa muddin kwamitin sulhu suka iso jiharsa, sai dai ayi ta ta qare, ya kumma qara da cewa: "A shirye nake a kaini kabari na, in Oshiomhole ya isa to ya aiko kwamitin..."

DUBA WANNAN: Yadda yara suka kashe Mamman Nur na Boko Haram

Ya ci gaba da cewa, su a jiharsu ba'a a yi musu dauki dora ba, ba kuma zasu bari a shigo musu jiha ba. Har ma da ashar, inda yake cewa in uwatar da uba nai sun haife shi to ya aiko su ya gani.

Gwamna Yari dai yana son ya dora wani na hannun damansa ne, inda shi kuma Adams Oshiomhole ke son saka wanda Abuja ke so.

INEC dai ta rufe kofar takara babu ko dan APC cikin wanda ya sami shiga takardar ballot a jihar, sai dai tace a je kotu.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel