EFCC ta kulle mataimakin Darakta, kan damfarar N145m

EFCC ta kulle mataimakin Darakta, kan damfarar N145m

- Ofishin yaki da rashawa ta maka wani mataimakin Darakta kotu

- Ana zargin shi da satar Naira miliyan 145,342,063

-Laifukan shi sun hada da hada kai ayi cuta, waskar da kudade da satar kudi

EFCC ta kulle mataimakin Darakta, kan damfarar N145
EFCC ta kulle mataimakin Darakta, kan damfarar N145
Asali: Facebook

Ofishin yaki da rashawa na jihar Legas a ranar juma'a sun maka Bello Na'Allah Yabo, mataimakin daraktan bangaren kudi na ma'aikatar al'amuran yan sandan kotu, gaban mai shari'a A.I Ogunmoye na babban kotun jihar dake Ado Ekiti, jihar Ekiti.

An gurfanar dashi ne sakamakon laifuka 13 wanda suka hada da hada kai dashi gurin cuta, waskar da kudade da satar kudi har Naira miliyan 145,342,063.

Yabo na fuskana shari'a ne tare da Imrana Ventures wanda shima ake zargi da amfani da tsohon matsayin shi na jami'i mai biyan kudi na yan sandar jihar Ekiti a 2015 wajen waskar da kudaden don amfanin su.

Wanda ake zargin ya boye laifin shi ta hanyar amfani da asusun bankin shi dake Unity Bank.

DUBA WANNAN: Zargin wai NPA ta boye N177b daga gwamnatin Tarayya; NPA tayi bayani dalla-dalla

Wanda ake zargin ya musa zargin da ake mishi. A sakamakon haka lauyan masu karar, George Chia-Yakua ya roki da a dage sauraron kara tare da tsare wanda ake zargi a gidan kaso.

Lauyan wanda ake kara, Y. C Maikyau, ya roki kotu da ta bada belin wanda ake karar.

Amma lauyan masu karar ya soki bada belin gani da cewa wanda ake karar bai aje komai gaban kotu ba da zai sa a bada belin. A don haka kada kotu ta dubi wanda ake kara da zancen belin.

Mai shari'a ya dage sauraron shari'ar zuwa 22 da 23 ga watan Janairu tare da belin a ranar 6 ga watan Disamba.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel