Kashe-kai ya ragu matuka ainun a duniya, an kuma gano dalilan hakan

Kashe-kai ya ragu matuka ainun a duniya, an kuma gano dalilan hakan

- Dalilin da yasa yawan kisan kai-da-kai ya ragu a duniya

- Raguwar ta faru ne musamman a matan kasar China da India

- Sharhi ne daga jaridar Economist ta Ingila

Kashe-kai ya ragu matuka ainun a duniya, an kuma gano dalilan hakan
Kashe-kai ya ragu matuka ainun a duniya, an kuma gano dalilan hakan
Asali: Instagram

Masana sunyi bayani akan yawa-yawan kashe kai da matasa keyi a duniya, an kuma tabbatar cewa hakan tafi bayyana a kasashen Asiya masu yawan jama'a.

A yanzu dai a duniya, wannan annoba ta ragu da kashi 29 cikin dari tun daga shekarar 2000 a kasashen Asiya. A cikin kasashen yammacin duniya kuwa, watau Turai da Amurka, ana samun raguwar kashe kai da kai tun a qarnoni da dama da suka gabata.

Misali: A Birtaniya, an samu kololuwar kunar bakin wake ne a 1934. Amma kuma a yanzu ana ta samun raguwar shi.

DUBA WANNAN: INEC na barazanar cire wasu jam'iyyu daga ballot

A China an fara samun raguwar ne a a karni na sha tara. Haka nan ma a kasashen Rasha, Japan, Korea ta kudu da India.

A Amurka kuwa ba haka bane, yawan kunar bakin wake karuwa tayi da kashi 18 cikin dari a wannan karnin. A yanzu da yawan kunar bakin wake a Amurka ta ninka ta China so biyu.

Raguwar kunar bakin wake ta tseratar da rayuka miliyan 2.8 tun daga 2000.

Wani kashin mutane sune masu matsakaicin shekaru a mazan kasar Rasha wanda dalilin shan giya ke kawo hakan.

Kashi na uku sune tsofaffi a fadin duniya.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng