'Yan Bindiga Sun Sake Ta'addanci, an Kashe Mutane da Sace Bayin Allah a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Sake Ta'addanci, an Kashe Mutane da Sace Bayin Allah a Kaduna

  • Wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun kai hari al’ummar Akwando da ke Kachia, inda suka kashe mutum biyu tare da sace wasu 20
  • Ƙungiyar Kuturmi Unity Development Association ta bayyana sunayen mutanen da aka yi garkuwa da su, tare da nuna damuwa kan yawaitar hare-hare a yankunansu
  • Ƙungiyar ta ce hare-haren da aka kai Ariko da Awon a baya sun yi sanadin mutuwar mutane da dama, ciki har da waɗanda suka mutu a hannun masu garkuwa da su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu 20 bayan kai hari al’ummar Akwando da ke Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna, ranar Laraba.

Harin, wanda rundunar ’yan sanda ba ta tabbatar da faruwarsa ba, ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na rana, kamar yadda shugabannin wata ƙungiyar al’umma suka bayyana.

Kara karanta wannan

Da gaske gwamnatin tarayya ta kulla yarjejeniyar tsaigaita wuta da Boko Haram

'Yan bindiga sun yi kisa a Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce shugaban ƙungiyar Kuturmi Unity Development Association, Dakta Joseph Ariko, tare da sakataren yaɗa labaranta, Manasseh Samuel Akwando, ne suka sanar da lamarin ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamban 2026.

Ƙungiyar ta nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da kashe mutane da yin garkuwa da su a al’ummomin Kuturmi.

Ta ce sabon harin ya faru ne a daidai lokacin da mazauna yankin ke ƙoƙarin farfaɗowa daga mummunan harin da aka kai al’ummar Ariko a ranar Lahadin Ista.

An bayyana sunayen waɗanda aka sace

A cikin sanarwar da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana harin a matsayin wani sabon abin damuwa da ya ƙara tsananta matsalar tsaro da al’ummominsu ke fuskanta.

Sanarwar ta ce:

"Abin takaici ne matuƙa ganin cewa harin ya faru ne a lokacin da al’ummarmu ke ci gaba da fama da illolin harin ranar Lahadin Ista da aka kai Ariko.”

Ƙungiyar KUDA ta kuma fitar da sunayen mutane 20 da rahotanni suka ce an yi garkuwa da su a harin na ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Ta'addancin 'yan bindiga ya ritsa da sojoji da mai juna biyu a Taraba

Sun haɗa da Usman Galadima, La’a’zarus Genesis, Madalin Markus, Happy Stephen, Lovet Ishaya, Afiniki Irimeya, Amina Ahmadu, Miracle Genesis, Hellen Irimeya da Musa Genesis.

Sauran sunayen su ne Janet Irimeya, Gloria Markus, Zila Stephen, Alis Ahmadu, Haske Ahmadu, Great Isiac, Hanatu Irimeya, Desmon Ishaya, Siam Shagari da Nansy Genesis.

An tuna da hare-haren Ariko da Awon

Ƙungiyar ta tuna cewa harin da aka kai al’ummar Ariko a ranar Lahadin Ista ya yi sanadin mutuwar mutane biyar a wurin da lamarin ya faru.

Ta ce wasu mutane 17 da aka yi garkuwa da su a harin sun mutu daga baya yayin da suke tsare a hannun masu garkuwa da mutanen.

Haka kuma, ƙungiyar ta nuna damuwa kan wani hari da aka kai al’ummar Awon, inda aka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu 11.

A cewar ƙungiyar, mutane biyar daga cikin waɗanda aka sace a Awon sun samu ’yancinsu a ranar 3 ga Nuwamban 2026.

Sai dai ɗaya daga cikinsu ya mutu washegari, yayin da wani mutum ya samu damar tserewa daga hannun masu garkuwa da shi.

Kara karanta wannan

EFCC ta bankado haramtacciyar matatar mai ta 'yan kasar waje cikin daji

Ƙungiyar ta ƙara da cewa sauran mutane biyar sun mutu ne a lokacin da suke tsare a hannun waɗanda suka sace su.

Hare-haren da aka kai Akwando, Ariko da Awon sun ƙara jawo hankalin jama’a kan matsalar tsaro da ke addabar al’ummomin yankin Kachia.

'Yan bindiga sun sace mutane a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun kaahe soja

A wani labarin kuma, kun ji cewa yan bindiga sun kashe soja, mafarauci da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Sarkin Yamma, kusa da yankin Jeb-Jeb da ke Ƙaramar Hukumar Karim-Lamido ta Jihar Taraba.

Maharan sun kuma harbi wani soja tare da jikkata shi, sannan suka yi awon gaba da wasu mazauna yankin bayan kai harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng