An Faɗi Girman Darajar Digirin da Tinubu Ya Gama da Shi a Jami'ar Amurka
- Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya kammala karatun digirinsa na lissafin kuɗi da daraja ta farko a jami’ar Chicago
- Alausa ya ce ya shafe kusan shekaru 30 yana zaune a Chicago, kuma ya san mutanen da suka yi karatu tare da Tinubu
- Sai dai bayanan jami’ar sun tabbatar da cewa Tinubu ya karanci lissafin kuɗi, ba tare da bayyana matsayin darajar digirin da ya samu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya kare tarihin karatun Shugaba Bola Tinubu, inda ya dage cewa shugaban ya kammala jami’ar Chicago da digirin farko mai daraja ta musamman.
Alausa ya ce Tinubu ya samu digirin farko a fannin lissafin kuɗi (Accounting) daga jami’ar da ke Amurka.

Source: Facebook
Jami'ar da Tinubu ya yi karatu

Kara karanta wannan
Gwamna ya yi magana mai zafi kan harin da aka kai wa ayarin Peter Obi da Kwankwaso
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television ranar Talata, 3 ga watan Nuwamban 2026.
Ya ce ya san jami’ar sosai saboda ya zauna a birnin Chicago na kusan shekaru 30, kuma ya taɓa ganawa da mutane da dama da suka yi karatu tare da Tinubu.
Da aka tambaye shi ko ya taɓa haɗuwa da abokan karatun shugaban ƙasar, Alausa ya amsa da cewa ya haɗu da da yawa daga cikinsu.
Ministan ilimi ya dage kan darajar digirin Tinubu
Da aka tambayi Alausa ko da gaske Tinubu ya kammala jami’ar da digirin farko mai daraja ta musamman, ministan ya amsa da cewa, tabbas, a fannin lissafin kuɗi.
Haka kuma, ministan ya bayyana Tinubu a matsayin ƙwararren mutum mai hazaka sosai, inda ya ce bai kamata a yi shakkar ƙwarewar shugaban ƙasar ba.
Alausa ya kuma kare ayyukan gwamnatin Tinubu, yana mai cewa shugaban ya sauya Najeriya daga ƙasar da ta durƙushe zuwa ƙasar da tattalinta ke samun ci gaba.
Sai dai mai gabatar da shirin ya tunatar da shi cewa akwai yara da dama da ba sa zuwa makaranta, yayin da talauci ke ci gaba da addabar al'umma.
Alausa ya ce bai kamata a karkatar da tattaunawar daga nasarorin da Tinubu ya samu ba, yana mai jaddada cewa shugaban ya yi wa Najeriya abubuwan alheri.

Source: Facebook
Abin da takardun jami’ar Chicago suka nuna
Batun cancantar karatun Tinubu ya daɗe yana jawo ce-ce-ku-ce, musamman bayan takaddamar da ta biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.
A watan Agustan 2026, batun ya sake tasowa bayan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara baje kolin takardun cancantar 'yan takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2027.
Wani takardar Tinubu mai lamba EC9 da jaridar Punch ta nuna cewa ya samu digirin farko a fannin Gudanar da Kasuwanci (Business Administration) daga jami’ar Chicago.
Takardar ta nuna cewa an ba shi digirin ne ranar 22 ga watan Yunin 1979, tare da rubuta cewa ya kammala karatun da karramawa.
Haka kuma, takardar ta ƙunshi shaidar kammala bautar ƙasa (NYSC), inda bayanai suka nuna cewa Tinubu ya yi hidimar ƙasa a jihar Oyo daga Disamban 1982 zuwa Nuwamban 1983.
Tinubu ya yi tukin tasi a Amurka
Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ya taba tukin tasi da wasu ayyuka a Amurka domin samun kudin biyan kudin karatunsa a jami'a.

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi II ya kuma magana, ya ba Tinubu shawarar da za ta taimaki gwamnatinsa
Tinubu ya ce kalubalen da ya fuskanta wajen neman ilimi sun yi tasiri kan manufofin gwamnatinsa na tallafa wa dalibai.
Shugaban ya ce NELFUND ta raba sama da Naira biliyan 372 ga dalibai, yayin da gwamnati ke gyara makarantun likitanci 24.
Asali: Legit.ng
