Ko kunsan nawa jihar Kano ke kashewa kan albashi kadai a kowanne wata?

Ko kunsan nawa jihar Kano ke kashewa kan albashi kadai a kowanne wata?

- Jihar Kano tana kashe naira biliyan 9.6 a duk wata

- Jihar na da ma'aikata 185,000 a karkashin ta

- Gwamnatin tana kokarin biyan ma'aikata albashin su akan lokaci

Ko kunsan nawa jihar Kano ke kashewa kan albashi kadai a kowanne wata?

Ko kunsan nawa jihar Kano ke kashewa kan albashi kadai a kowanne wata?
Source: Facebook

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jihar tana biyan ma'aikata naira biliyan 9.6 a duk wata.

Ganduje ya bayyana haka ne a yayin taron ma'aikatan kananan hukumomi 44 karkashin NLC wanda ya gudana a Mambayya house a ranar Alhamis.

Shugaban ma'aikata Auwal Muhammed wanda ya wakilci gwamna Ganduje a wajen taron yace gwamnatin jihar Kano tana iya biya ma'aikatan ta albashi akan lokaci wanda hakan ba karamar nasara bace.

DUBA WANNAN: Khashoggi: Shugaban Rasha zai tattauna da Yarima bin Salman a fadar Kremlin

Ya kara da cewa a jihar Kano munada ma'aikata wanda yawan su yakai 185,000 wanda suke karkashin gwamnatin sannan aduk wata ana biyansu albashi jimillar N9.6b.

Ya kara da cewa jihar tana iya biyan albashi sabanin wasu jihohin da sai sun nemi bashi kafin su biya ma'aikata.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel