Khashoggi: Shugaban Rasha zai tattauna da Yarima bin Salman a fadar Kremlin

Khashoggi: Shugaban Rasha zai tattauna da Yarima bin Salman a fadar Kremlin

- Shugaban kasar Russia zai gana da Yarima MBS a bisa kashe dan jarida da akayi

- A watan daya gabata ne dai aka kashe wannan dan jarida

- Shugabannin biyu zasu tattauna akan lamarin kasuwancin mai

Khashoggi: Shugaban Rasha zai tattauna da Yarima bin Salman a fadar Kremlin

Khashoggi: Shugaban Rasha zai tattauna da Yarima bin Salman a fadar Kremlin
Source: Depositphotos

A ranar Laraba ne aka bayyana cewa Shugaban kasar Russia Vladmir Putin, Zai gana da takwaransa na Masaautar kasar Saudiyya, Yarima mai jiran Gado Muhammadu dan Salmanu a kasar su ta Rasha, a Kremlin, fadar shugaban kasa.

Shugabannin biyu zasu tattauna akan sha'anin kasuwancin mai da kuma sabani da ake samu da juna kan kasar Syria da ma yaki da ISIL.

A watan daya gabata ne aka kashe dan jaridar mai suna Jamal Khashoggi wanda aka nemi shi aka rasa kafin daga bisani aka tabbatar Saudiyya ce ta hallaka shi.

DUBA WANNAN: Duniya tayi Allah-wadai da Saudiya bayan da ta dawo da littafan zafafa ra'ayi a makarantun ta

Kasashen duniiya dai, sun saka ma kasar Saudiyyar matson lamba kan sai an fadi ko wanene ya sanya ayi kisan na rashin tausayi, da ma kuma a hukunta ko waye.

Da yawa suna ganin babu wanda zai sa ayi wannan mugun aiki, sai dai kuma, kasar ke baiwa duniya mai, kuma babu alamar a'a iya sanya musu takunkumi.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel