Dalla-dalla: Yadda aka fanso tagwayen Zamfara

Dalla-dalla: Yadda aka fanso tagwayen Zamfara

- Yanda aka fanso wasu yan Biyu da akayi garkuwa dasu

- An jima ana bibiyar tagwayen kafin a samu damar sace ce

- Masu garkuwar sunyi duba da yawan magoya baya da tagwayen ke dasu a shafukan su na sadarwa

Dalla-dalla: Yadda aka fanso tagwayen Zamfara

Dalla-dalla: Yadda aka fanso tagwayen Zamfara
Source: Facebook

Masu garkuwa da mutanen sun nemi a basu naira miliyan goma sha biyar (N15m) wanda da taimakon al'ummar Najeriya da kuma Sanata Kabiru Marafa aka samu aka hada kudin.

Bayan kammaluwar kudaden Ibrahim wanda ya kasance miji ga yayar wadannan tagwaye ya kira masu garkuwar ya bayyana musu cewa kudi fa sun hadu inda suka nemi da akai musu kudin wani gari mai suna Gurbin Burai.

Daga nan ne sukace su karasa wani kauye mai suna Dumburum wanda daganan suka shiga daji inda anan ne suka samu nasarar karbo wadannan yara.

Rahoton ya bayyana cewa masu garkuwar sun dade suna bibiyar wadannan tagwaye kafin su samu damar sace su.

DUBA WANNAN: Duniya tayi Allah-wadai da Saudiya bayan da ta dawo da littafan zafafa ra'ayi a makarantun ta

Sannan sunyi la'akari da dumbin magoya baya da suke dasu a shafukan su na sadarwar zamani.

Masu garkuwar sun samu nasarar sace wadannan yan mata a lokacin da suka ziyarci kauyen mahaifinsu da niyyar kai musu katin bikin su.

Ya kamata masu dora hotunan su a social media su hankalta saboda sabon tsarin da masu garkuwa da mutane suka fito dashi na la'akari da yawan masoyan ka a social media.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel