Muhimman abubuwa 7 da Buhari ya fadi a Maiduguri

Muhimman abubuwa 7 da Buhari ya fadi a Maiduguri

A ranar Laraba 28 ga watan Nuwamba ne shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da taron hafsin hafsoshin Najeriya na 2018 wadda aka saba yin duk shekara. Wannan karon an gudanar da taron ne a birnin Maiduguri na jihar Borno. Legit.ng ta kawo muku muhimman abubuwa bakwai da shugaban kasan ya fadi.

Muhimman abubuwa 7 da Buhari ya fadi a Maiduguri

Muhimman abubuwa 7 da Buhari ya fadi a Maiduguri
Source: Twitter

Ga abubuwan da shugaban kasa ya fadi a jawabinsa:

1. Jami'a da dakarun sojojin da ke yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a Arewa maso gabas suna bukatar dukkan shugabanni su mayar da hankali a kansu.

2. A matsayi na na shugaban ka, ina iya kokari na domin ganin kowanne dan kasa ya samu tsaro. Domin cimma wannan burin dole dukkan hukumomin tsaro sun yunkuro domin magance matsalar rashin tsaro a kasar.

3. Samar da tsaro yana daya daga cikin abubuwan da gwamnati na ta mayar da hankali a kai. Hukumar Sojin Najeriya tayi nasarar kwato garuruwa da dama da suke hannun 'yan ta'adda tare da ceto mutane da yawa da akayi garkuwa da su da samar da zaman lafiya a yankin na Arewa maso gabas.

DUBA WANNAN: 'Yan majalisar dokokin jihar APC sun tafi yajin aiki saboda rashin biyansu alawus

4. Hukumar Sojin Najeriya sun kawo zaman lafiya a yankin Niger-Delta da wasu sassan kasar da ake fama da rikici tsakanin makiyaya da manoma.

5. Ya zama dole in jinjinawa dakarun Sojin kasar nan wadanda suka sadaukar da kansu wajen tabbatar da cewa an samu zaman lafiya a sassan kasan nan daban-daban.

6. Na san cewa wasu daga cikin sojojin mu sun rasa rayyukansu yayin yaki da ta'addanci. A yayin da muke tunawa da su kuma muke mika ta'aziyya ga iyalensu, ina son mika godiyar gwamnati da al'ummar Najeriya ga sojojin da suka rasu da iyalensu saboda jarumtakar da su kayi. Muna kuma mika ta'aziya ga sauran mutane suka rasa 'yan uwa a rikicin Boko Haram da ma wasu rikice-rikicen.

7. A yanzu da babban zaben 2019 ke karatowa, ina kira da dukkan hukumomin tsaro su dage wajen gudanar da ayyukansu ba tare da nuna fifiko ga kowane jam'iyya ba. Kazalika, ya kamata ku sanya idanu yayin zaben domin ganin cewa babu wani rikici da ya barke kamar yadda ka'idojin aikin ku ya tanada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel