Galadima ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar ACPN

Galadima ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar ACPN

'Yar takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar ACPN, Obi Ezekwesili, ta zabi Ganiyu Galadima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Hakan na kunshe ne cikin wata wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar bayan kammala wani taro a Otal din Kwara da ke garin Ilorin a jihar Kwara.

Kafin zabensa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa, Ganiyu ya kasance shugaban jam'iyyar ACPN na kasa.

Kazalika ya taba zama dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar a shekarar 2015.

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar a jiya, Talata, ne kungiyar matasan kabilar Igbo (Ohanaeze Youth Council) ta nemi dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da ya fito fili da zuciya daya ya fadi zangon mulki nawa yake son yi idan ya lashe zaben shekarar 2019.

A jawabin kungiyar mai dauke da sa hannun Mazi Okwu Nnabuike, sakataren kungiyar, matasan sun ce akwai alamun yaudara a alkawuran da Atiku ya dauka domin ya debi tsawon shekaru 6 kafin ya cika su bayan kuma ya bayyana cewar zangon mulki data kawai zai yi.

Galadima ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar ACPN
Galadima da Ezekwesili
Asali: Twitter

Kungiyar matasan ta ce kamata ya yi kujerar shugaban kasar Najeriya ta juya zuwa yankinsu a shekarar 2023 tare da bayyana cewar Atiku ba zai samu goyon bayan 'yan kabilar Igbo ba matukar bai alkawarin barin mulki bayan kammala zango daya a mulki ba.

DUBA WANNAN: Kotu ta daure shugaban hukumar UBEC, Murtala Adamu, shekaru 41 a gidan yari

Kungiyar ta yi kira ga jama'ar yankin kudu maso arewa da su yi karatun ta natsu kafin zaben shekarar 2019 domin gudun shiga halin da gwamnonin yankin kudu maso yamma su ka shiga a shekarar 2003 bayan goyawa Obasanjo baya kuma daga baya ya maye gurbin jam'iyyar su ta AD da PDP.

Matasan sun yi alkawarin tabbatar da cewar sun kayar da duk gwamnan yankin da bai goyi bayan bukatar 'yan kabilar Igbo ba.

"Kuri'un 'yan kabilar Igbo dake fadin kasar nan ne zasu nuna waye zai zama shugaban kasa a shekarar 2019.

"Mun yi nazarin alkawuran kamfen din Atiku da yake sa ran kammala su cikin shekaru 6. Muna bukatar Atiku ya fito fili da zuciya daya ya dauki alkawarin cewar zangon mulki daya zai yi matukar yana son kuri'ar 'yan kabilar Igbo," a cewar kungiyar ta OYC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel