Yanzunnan: Shugaba Buhari ya rage kudin makaranta na JAMB da NECO don dalibai

Yanzunnan: Shugaba Buhari ya rage kudin makaranta na JAMB da NECO don dalibai

- Shugaba Buhari ya rage kudin JAMB

- An gano JAMB tana tara kudi biliyan tara

- A baya N60m kadai suke kawo wa

Yanzunnan: Shugaba Buhari ya rage kudin makaranta na JAMB don dalibai

Yanzunnan: Shugaba Buhari ya rage kudin makaranta na JAMB don dalibai
Source: Facebook

Bisa dalilin gano cewa kudin jarrabawar JAMB yayi wa talakawa tsada, kuma an habaka yawan kudaden da ofishin ke tarawa, daga N60m zuwa N9b, fadar shugaban kasa ta ce zata rage kudin JAMB don kowa ya samu ya shiga makaranta.

A tsari dai, ofishin jarrabawar ba wai an yi shi bane domin a ci riba, a'a sai dai an yi ofishin ne don a samar da kudin tsari da tafiyar da ma'aikatar.

An nemi hukumar Jamb data biya yan bautar kasa N9b. A lokacin da aka kirani aka cewar ana bukatar N300 daga ofishina nayi matukar mamaki.cewar Oloyede. Ya zama lallai yan Najeriya su mike don yakar cin hanci da rashawa a kasar.

Rijistara na Jamb Prof Ishaq Oloyede yace cin hanci da rashawa yana kara samun wajen zama a kasar nan.

Olayede yace yayi matukar mamaki da aka nemi hukumar ta Jamb data samar wa da yan bautar kasa kudi kimanin N9b.

Rijistaran ya bayyana haka ne a ranar Talata a yayin dibar sabbin malamai a jami'ar Tai Solarin dake jihar Ogun.

Olayede yace a lokacin da ministan kudi ya kirashi a wayar salula yake ce masa ana bukatar hukumar ta samar da N200b ko 300b yayi matukar firgita dajin wannan batu duba da halin da hukumar da tsinci kanta a ciki.

DUBA WANNAN: Jonathan ma yaci kudin OML 245 ashe

Ya bayyana cin hanci a matsayin abinda ya hana kasar nan ci gaba.

Bana ganin mutuncin mutane da dama wadanda kuke gani a manya manyan motoci saboda inada masaniya dangane dasu.

Sannan ministan ilimi ya kirani yana bukatar ofishin daya bawa gwamnatin tarayya N500b.

Abin mamaki gwamnatin tana bukatar kudi wanda jimillar su yakai 9b daga ofishin na Jamb wanda wannan batu yake hanani bacci kullum a hanyar bincike make domin in gano inda matsalar dake.

Amma abin tambayar anan shine me kasar zatayi da wadannan makudan kudade?

Ya zama lallai yan Najeriya su mike tsaye don yakar cin hanci da rashawa a fadin kasar nan.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel