Harin Metele: Yadda na tsira da raina - Sojan Najeriya

Harin Metele: Yadda na tsira da raina - Sojan Najeriya

Wani sojan Najeriya da ya samu damar tsira da ransa a harin da mayakan kungiyar Boko Haram su ka kai sansanin soji dake garin Metele a karamar hukumar Guzamala, jihar Borno, ya bayar da labarinsa.

A cewar wani rahoton yanar gizo da wani mai suna Barista CJ ya wallafa, ya bayyana cewar sojan mai suna Gboy Nick ya ce ya shiga halin dimuwa yayin da mayakan Boko Haram ke tunkarar sansanin su bayan dukkan alburusan dake hannunsa sun kare.

Sojan ta bayyana cewar ya kasa tashi ya gudu duk da mayakan Boko Haram na tunkarar sansanin bayan fahimtar cewar sun ci karfin sojojin Najeriya.

Harin Metele: Yadda na tsira da raina - Sojan Najeriya
Sojojin Najeriya
Asali: Twitter

Soja ya bayyana cewar ya buya a bayan wata duhuwa rike da wukar sa a hannu yana jiran abokin mutuwa.

DUBA WANNAN: Zan yi murabus idan APC ta lashe zaben jiha ta - Babban Sarki a arewa

Rahoton ya yi bayanin yadda sojan ya samu nasarar kashe karin wani dan Boko Haram guda daya da ya zo kusa da shi cikin rashin sani tare da daukan bindigar sa, wacce ya yi amfani da ita wajen cigaba da harbi ba kakkautawa domin razana ragowar mayakan kungiyar Boko da ke kara tunkaro sansanin.

Gboy ya kara samun nasarar harbe wasu 'yan Boko Haram 4 kafin daga bisani ya samu sukunin guduwa wata maboya da wasu sojoji su ka fake.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng