Har yanzu duniya na qara Allah wadai da kisan da Boko Haram suka yi wa sojin Najeriya
- Majalisar dinkin duniya ta tur da harin da boko haram ta kaiwa sojojin Najeriya
- Ta mika sakon ta'azziya ga Najeriya da iyalan wadanda rasu
- Sun shirya kai hare hare a gurare da dama bayan Matele

Asali: UGC
Sakataren Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres yayi tur da harin da boko haram ta kaiwa sojojin Najeriya musamman a jihar Borno.
Guterres ya mika sakon ta'aziyyar sa ga Najeriya da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukan su.
A satin daya gabata ne aka kaiwa sansanin sojin Najeriya dake Matele hari inda sojoji da dama suka rasu.
DUBA WANNAN: Kada ka sake ka leko mana qasa, an gargadi Yariman Saudiyya kan taron G20
Majalisar tace rahoto ya bayyana cewa sun shirya kai hare hare a gurare da dama bayan Matele.
Shugaban kasa Muhammad Buhari yayi kokari wajen kawo karshen masu kai hare hare a arewa maso gabacin kasar nan wanda boko haram suka kafa shekaru 10 da suka wuce.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng