Martanin APC ga PDP: Buhari baya tsoron muhawara da Atiku don 2019
- Buhari yanajin tsoron yin muhawara cewar jam'iyar PDP
- Har zuwa yanzu shugaban kasar bai yanke hukunci ba akan wannan muhawara
- Jam'iyar PDP ta saba gujewa muhawara

Asali: UGC
Hukumar dake kula da kamfen din shugaban kasa Muhammad Buhari tace Shugaban baya tsoron gabatar da muhawara matukar matakan muhawarar da kuma sharadan ta sunyi daidai.
Jam'iyar PDP ta bukaci Shugaban kasar da suyi wata muhawara da dan takarar ta Atiku Abubakar akan zaben Shugabancin kasa na shekara ta 2019.
Jam'iyar tace Shugaban yanajin tsoron gudanar da wannan muhawara da aka shirya gudanar wa aduk inda ya zabar musu.
A jiya ne hukumar dake kula da kamfen nasa ta maidawa PDP martani.
Mai magana da yawun hukumar Festos Keyamo SAN yace PDP ce take tsoron wannan gwabzawa da za'ayi.
Yace Shugaban kasar zai fitar da lokaci ne bayan ya duba sharudan wannan muhawara.
DUBA WANNAN: Cikin minti bakwai kacal aka kashe Khashoggi
Keyamo ya kara da cewa "ba sabon abu bane a wajen PDP don ta gujewa wannan muhawara duba da yanda Obasanjo ya gudu,Goodluck ma ya gudu saboda haka jam'iyar tana da tarihin gujewa muhawara".
Ya kara da cewa har zuwa yanzu hukumar bata da masaniya akan muhawarar masu takarar shugabancin kasa amma da zarar sun samu bayani zasu yanke hukuncin yi ko kuma akasan haka.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng