Bangaren sharia na kasar nan na barazanar shiga yajin aiki suma

Bangaren sharia na kasar nan na barazanar shiga yajin aiki suma

- Kungiyar ma'aikatan kotun Najeriya, reshen jihar Nasarawa sun Zargi Kamashon ma'aikatar shari'ar jihar da laifin bacin suna

- Sanarwa ce akan hukuncin ma'aikatan wanda suka ce ba bisa ka'ida bane

- Kamashon ma'aikatar shari'a tace babu bukatar kungiyar da ba a biya ba

Bangaren sharia na kasar nan na barazanar shiga yajin aiki suma
Bangaren sharia na kasar nan na barazanar shiga yajin aiki suma
Asali: UGC

Kungiyar ma'aikatan shari'a ta Najeriya, reshen jihar Nasarawa ta zargi kamashon ma'aikatar shari'ar da bata musu suna ta dalilin wata sanarwar gidan rediyo da tayi akan yajin aikin kungiyar ba bisa ka'ida bane.

Kungiyar na maida martanin sanarwa da gidan rediyon Nasarawa yayi.

Anyi sanarwar ne bayan taron ofishin ma'aikatar shari'ar jihar da akayi a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2018 inda tace babu bukatar kungiyar da ba a biya ba.

DUBA WANNAN: Kada ka sake ka leko mana qasa, an gargadi Yariman Saudiyya kan taron G20

Kungiyar ta kara da cewa babu wani rashin jituwa tsakanin kungiyar da hukumar, kari da cewa babu bukatar wani yajin aiki tunda kungiyar bata bada sanarwar cewa zata tafi yajin aiki ba.

Amma shugaban kungiyar ma'aikatan shari'ar, reshen jihar Nasarawa, Comrade Jimoh Musa yace sanarwar ma'aikatar shari'ar ya sha bamban kuma abin mamaki ne saboda sun bada wasikar tunatarwa a ranar 8 ga watan Fabrairu, 2018 akan zata tafi yajin aiki in har baa biya musu bukatar su ba.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng