Kamar a fim: Da saurayinta yaga bill din abincin da suka ci ya kai N83,000 sai ya tsere ya barta
- Soyayya a Najeriya akwai tsada, inda mata suka zama masu idon cin naira
- Maza na iya bakin qoqarinsu, amma wasu lokutan sukan dan hada da qarya
- Yanzu dai budurwar ta kira a zo a cece ta hannun masu gidan abinci

Asali: Instagram
Dirama ta qarke agidan abinci watau Restaurant, tsakanin wata budurwa da zamu kira da Balkisa, don sakaya sunanta saboda tsaro da sirri. Inda zamu kira saurayin da Muzambilu.
Watau dai Muzammil ya dauki Balki don fita yawon shaqatawa, inda ya kaita gidan abinci na alatu, mai kama da su Mista Biggs ko Chicken Republic.
Sai dai budurwa Balki, ta shaqo inda Muzambilu baya iya karya, bayan da ta ci abinci da kayan kwalam da makwalashe na kusan N100,000, albashinsa kenan kacokan na wata, kuma ba'a ma yi ba sai litinin.
Koda ya qyalla ido ya ga yawan bill din sai yace bara yaje mota dauko atm dinsa ya dawo, zumbur kuwa ya tashi, ya fice, shiru-shiru bai dawo ba.
DUBA WANNAN: Kada ka sake ka leko mana qasa, an gargadi Yariman Saudiyya kan taron G20
Da aka gaji da jira aka duba sai aka ga sam baya waje, babu motarsa, wayarsa kuwa a kashe.
Da ta duba tata wayar, Balkisa sai taga ya bar mata sakon tes, na cewa tayi hakuri, domin shi fa ya samfe, don wallahi bashi da wannan kudin.
Zata fita, Sakyurate na Restoran suka ce a'a, ta dai zauna, don sai ta biya wannan kudi zasu barta ta tafi.
Majiyarmu tace mana yanzu dai budurwa Balkisa, tana can hannun ma'aikata, inda ta auno saqo da 'yan Najeriya na kusa ko na nesa, ta shafinta na tuwita, da su agaza mata suzo su biya mata wannan kudi, don ta fita daga hannun masu abinci.
Su kuma samari da ma 'yan mata, na can sunyi mata caa, suna suburbudarta wai ta fiye zalama da ma qarya, sunce laifinta ne da ta tara wannan bill. Wasu kuwa suna ganin Muzambilu mai laii, don shine ya shirga mata qarya, ta dauka ko dan minista ne.
Jama'a sai a taimaka, ga sunan shafin nata: @browncandyx, ko akwai mai niyya.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng