Cin mutuncin yan Arewa da Hausa Fulani ne: ra’ayin Kwankwaso game da bidiyon Ganduje

Cin mutuncin yan Arewa da Hausa Fulani ne: ra’ayin Kwankwaso game da bidiyon Ganduje

Tsohon gwamnan jahar Kano, kuma mamba a majalisar dattawan Najeriya dake wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana damuwarsa da fitar faya fayan bidiyon dake bayyana gwamnan jahar Kano yana karbar rashawa.

Legit.com ta ruwaito Kwankwaso ya bayyana haka ne cikin hira da yayi da wata gidan rediyo dake jahar Kano, inda ya bayyana cewa yana da labarin yunkurin sakin bidiyon, amma yayi iya bakin kokarinsa akan kada a sakesu domin wasu dalilai.

KU KARANTA: Bani na baiwa EFCC kyautan naira miliyan goma ba – Gwamna Ganduje

A cewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bai bada goyon bayan sakin bidiyon bane saboda hakan zai zamto tamkar cin mutunci ko cin fuska da miliyoyin jama’an yankin Arewacin Najeriya da ma al’ummar Hausa Fulani gaba daya a duk inda suke.

Cin mutuncin yan Arewa da Hausa Fulani ne: ra’ayin Kwankwaso game da bidiyon Ganduje
Kwankwaso
Asali: UGC

“Na samu labarin bidiyon tun kafin a sakesu, kuma na kira masu abin na shawarcesu kada su yi abinda suke nufi, domin kuwa bidiyon cin fuska ne ga jahar Kano, Hausa Fulani, Yan Arewa da ma Musulman duniya gaba daya.” Inji Kwankwaso.

Sanatan ya kara da cewa dalili na biyu da yasa bai goyi bayan a saki bidiyon ba shine don kasancewa a lokacin suna rigimar fitar da dan takarar gwamna a jam’iyyarsu ta PDP ne, don haka sai a ga kamar da hannunsu aka fitar don su bata ma gwamnan suna su kadashi zabe.

Daga karshe Kwankwaso yace: “Bana goyon bayan sakin bidiyon saboda ba iya gwamnan bidiyon za ta taba ba, hatta iyalasan sai ta shafesu da ma kafatanin al’ummar jahar Kano gaba daya.”

A wani labarin kuma Kwankwaso yace Buhari bashi da cikakken sahihin bayani game da zargin da ake yi masa na cewa wai ta saci kudade a yayin da yake gwamnan jahar Kano, a cewar Kwankwaso, Buhari bai san komai ba game da Kano.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng