Dubun wasu matasa maza dake neman manyan mutane a Kano da lalata ta cika, hoto

Dubun wasu matasa maza dake neman manyan mutane a Kano da lalata ta cika, hoto

- Hukumar 'yan sanda a jihar Kano ta bayyana cewar ta kama wasu gungun matasa dake sana'ar karuwanci da manyan mutane a birnin Kano

- Magaji Majiya, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kano, ce matasan na yawon neman lambar wayar manyan mutane a garin Kano domin kulla alakar luwadi da su

- Kazalika ya bayyana cewar matasan kan nemi kudi daga hannun duk wani babban mutum da ya ki amincewa da su, ta hanyar yi masu barazanar zasu tona masu asiri

Hukumar 'yan sanda a jihar Kano ta bayyana cewar ta kama wasu gungun matasa dake sana'ar karuwanci da manyan mutane a birnin Kano.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya, ya ce matasan da su ka kama su ne; Suraja Shehu, mazaunin layin Lale Cinema dake unguwar Goron Dutse, da Yahaya Sharif, mazaunin unguwar Rijiyar Lemo.

Ya ce matasan na yawon neman lambar wayar manyan mutane a garin Kano domin kulla alakar luwadi da su tare da yiwa duk wanda ya ki amincewa da su sharri.

Dubun wasu matasa maza dake neman manyan mutane a Kano da lalata ta cika, hoto
Suraja da Yahaya
Asali: Twitter

Majiya ya kara da cewar matasan na watsa sakonnin bata suna a dandalin sada zumunta na Whatsapp a kan duk wani babban mutum da ya ki amincewa ya kulla alaka da su.

Kazalika ya bayyana cewar matasan kan nemi kudi daga hannun irin wadannan manyan mutane ta hanyar yi masu barazanar zasu tona masu asiri matukar basu ba su adadin kudin da su ka nema ba.

DUBA WANNAN: Daga na 1 zuwa na 6: An fara sayar da faifan bidiyon Ganduje na karbar dalolin

Tun a shekarun baya da su ka wuce majalisar dokokin Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari ga duk wanda aka samu da laifin yin auren jinsi ko yin soyayya tsakanin jinsi daya.

Sai dai duk da wannan doka hakan bai hana 'yan Najeriya; manya da matasa, maza da mata, kulla alakar soyayya tsakanin jinsi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng