Gwamna Yari ya dakatar da sarakuna hudu a Zamfara
Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da wasu masu rike da sarautun gargajiya guda hudu a jihar da ake zargi da hannu wajen hadin baki da 'yan bindiga da ke kashe-kashe a jihar.
Kwamishinan Kananan hukumomi da harkokin sarauta, Alhaji Bello Dankande ne ya bayar da sanarwan ranar Litinin a Gusau yayin wani taron manema labarai da ya kira.
Ya ce wadanda aka dakatar sune Hakimin garin Gora da ke karamar hukumar Talata Mafara da kuma Musa Bariki, hakimin Barikin Daji.

Asali: Depositphotos
Saura kuma sun hada da dagatan garin Gyadi da Tungun Dutsi duk a karamar hukumar Bukkuyum da ke jihar ta Zamfara.
DUBA WANNAN: Gwamnonin kabilan ibo sun mika bukatarsu ga shugaba Buhari
Kwamishinan ya ce dukkan masu sarautun gargajiyar hudu za su gurfana gaban wata kwamitin bincike na musamman kuma za a gurfanar da su a kotu idan aka gano suna da laifi.
Ya yi gargadin cewa gwamnatin jihar ba za tayi wata-wata ba wajen tsige duk wani basarake 'ba tare da la'akari da girmar kujerarsa ba muddin aka tabbatar yana hulda da 'yan bindiga ko miyagun mutane.'
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa jihar ta Zamfara tana fama da kallubalen tsaro na yan fashi da makami, garkuwa da mutane, kashe-kashen mutane da satan shanu musamman a kauyuka.
Majiyar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa kwamishinan ya yi bajekolin wasu bindigu hudu da aka kwato daga hannun wasu 'yan bindiga a kananan hukumomin Maru da Bukkuyum a jihar ta Zamfara.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng