Sojojin Najeriya sun tarwatsa 'yar kunar bakin wake, sun yi nasara kan 'yan ta'adda, hotuna

Sojojin Najeriya sun tarwatsa 'yar kunar bakin wake, sun yi nasara kan 'yan ta'adda, hotuna

- Dakarun sojin Najeriya su ka yi nasarar tarwatsa wata 'yar kunar bakin wake dake dauke da jigidar bama-bamai a jikinta

- Sojojin sun yi nasarar tarwatsa yarinyar ne yayin a garin Gulak a hanyarta ta zuwa kauyen DAR, inda take niyyar zuwa domin tayar da bama-baman

- A wani labarin kuma, dakarun soji sun tarwatsa sansanin 'yan ta'addar ne a yankin Katsina-Ala da Zaki Biam a jihar Benuwe

A yau, Litinin, ne dakarun sojin Najeriya su ka yi nasarar tarwatsa wata 'yar kunar bakin wake dake dauke da jigidar bama-bamai a jikinta.

Sojojin sun yi nasarar tarwatsa yarinyar ne yayin a garin Gulak a hanyarta ta zuwa kauyen DAR, inda take niyyar zuwa domin tayar da bama-baman.

A wani labarin mai nasaba da wannan, dakarun soji sun nasara a kan wasu 'yan ta'adda a jihar Benuwe.

Dakarun soji sun tarwatsa sansanin 'yan ta'addar ne a yankin Katsina-Ala da Zaki Biam a jihar Benuwe.

Ko a ranar asaba sai da Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar hedkwatar hukumar tsaro ta kasa ta bayyana cewar yanzu haka dukkan jama'ar da rikicin makiyaya ya shafa a jihar Benuwe sun koma gidajensu bayan ganin bayan 'yan ta'addar makiyaya da su ka addabi sassan jihar.

Sojojin Najeriya sun tarwatsa 'yar kunar bakin wake, sun yi nasara kan 'yan ta'adda, hotuna
"yan ta'addar Benuwe
Asali: Facebook

Sojojin Najeriya sun tarwatsa 'yar kunar bakin wake, sun yi nasara kan 'yan ta'adda, hotuna
'yan ta'addar Benuwe
Asali: Facebook

Sojojin Najeriya sun tarwatsa 'yar kunar bakin wake, sun yi nasara kan 'yan ta'adda, hotuna
Gawar 'yar kunar bakin wake
Asali: Facebook

John Agim, darektan yada labaran hukumar tsaro, ne ya sanar da hakan tare da sanar da cewar atisayen soji ne ya kawo karshen aiyukan ta'addanci na makiyayan.

A cewar sa, jami'an soji sun rushe duk wani sansanin makiyaya da ke fadin jihar ta Benuwe.

DUBA WANNAN: 'Yan kasuwar shanu 15 daga arewa sun mutu a hanyar su ta kai dabbobi kudu

Agim ya kara da cewar nasarar da atisayen dakarun soji ya samu bai tsaya iya jihar Benuwe, ya shiga har jihohin Nasarawa da Taraba, da ke makwabtaka da jihar Benuwe.

A cewar sa, babu wani sansanin makiyaya da ya rage a jihar Benuwe kuma tuni jama'ar da su ka gudu sun koma garuruwansu na kakanni da iyaye.

Kazalika, Agim ya ce dakarun soji sun yi nasarar rage aiyukan ta'addanci na kungiyoyin 'yan bindiga daban-daban da ke jihar Benuwe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng