'Yan kasuwar shanu 15 daga arewa sun mutu a hanyar su ta kai dabbobi kudu

'Yan kasuwar shanu 15 daga arewa sun mutu a hanyar su ta kai dabbobi kudu

A kalla 'yan kasuwar dabbobi 15 ne daga kauyen Maiyama, a jihar Kebbi, suka gamu da ajalinsu a yau, Lahadi, a wani hatsarin mota da ya ritsa da su a hanyar su ta zuwa kai shanu Legas.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar 'yan kasuwar daga garuruwan Andare, Katenga, da Maiyama, na hanyar su ta zuwa cin kasuwar shanu a jihar Legas lokacin da hatsarin ya ritsa da su.

Rahoton NAN ya bayyana cewar motar da ke dauke da 'yan kasuwar da shanunsu ta kwacewa direba a kan hanyar Maiyama zuwa Koko, sannan ta wuntsila zuwa cikin daji.

'Yan kasuwar shanu 15 daga arewa sun mutu a hanyar su ta kai dabbobi kudu
'Yan kasuwar shanu 15 daga arewa sun mutu a hanyar su ta kai dabbobi kudu
Asali: UGC

Wani shaidar gani da ido, Garba Maiyama, ya shaidawa NAN cewar, "mutane 15 daga cikin 'yan kasuwar dabbobin take su ka mutu kuma tuni aka mika su ga iyalansu domin yi masu jana'iza kamar yadda Musulunci ya tanada.

DUBA WANNAN: Kotu ta yankewa mamba a majalisar dokokin jihar Zamfara hukuncin daurin shekaru 4

"Babban abin tashin hankalin shine yadda a gida daya mutane 5 su ka mutu a hatsarin.

"Bamu san abinda ya haddasa hatsarin ba gaskiya," a kalaman shaidar.

Sai dai kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kebbi, DSP Danjuma Possy, ya shaidawa NAN cewar ya zuwa yanzu dai ba a sanar da su batun hatsarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng