Dalibai mata 3 sun mutu a makarantar kwana bayan cin kwadon rama

Dalibai mata 3 sun mutu a makarantar kwana bayan cin kwadon rama

A ranar Juma'a ne gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya kai ziyarar ta'aziyya da jaje a makarantar sakandiren 'yan mata ta kwana Maga inda wasu dalibai uku su ka mutu.

Shugabar makarantar sakandiren, Lami Abubakar, ta shaidawa gwamna Bagudu cewar daliban sun gamu da ajalinsu ne bayan cin wani abinci da aka hada da ganyen rama.

Lami ta bayyana cewar daya daga cikin daliban da su ka mutu ne ta zo da abincin daga gidansu.

Ba a bayyana sunayen yaran da su ka mutu ba ya zuwa yanzu.

Dalibai mata 3 sun mutu a makarantar kwana bayan cin kwadon rama
Gwamnan jihar Kebbi da shugabar makarantar yayin ziyarar ta'aziyya
Asali: Twitter

A wani labarin na legit.ng daga jihar Sokoto mai makwabataka da Kebbi, kun ji cewar gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya rantsar da Alhaji Mannir Dan'iya, a matsayin sabon mataimakinsa biyo bayan murabus din tsoho mataimakinsa, Alhaji Ahmed Aliyu, a ranar 13 ga watan Nuwamba.

Da yake jawabi yayin rantsar da sabon mataimakin a yau, Juma'a, Tambuwal ya ce har yanzu akwai kyakykyawar alaka tsakaninsa da tsohon mataimakin nasa.

DUBA WANNAN: Tsohon ministan PDP ya karbi kadarorinsa daga hannun EFCC bayan ya koma APC

"Akwai fahimtar juna tsakani na da tsohon mataimakina.

"Ina kira ga matasan jihar Sokoto da su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri'a ga jam'iyyar PDP a zaben 2019," a cewar Tambuwal.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar Aliyu ya yi murabus ne domin samun damar mayar da hankali a kan yakin neman zaben takarar kujerar gwamnan jihar Sokoto da ya ke yi a jam'iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel