Sun kuma! Boko Haram sun tare sojojin dake kwashe kayan aiki daga Metele, sun kwashi makamai
- Gawarwakin har sun ffara rubewa ba'a gama kwasowa ba
- A makon jiya aka kai harin kan soji a Metele
- Sun sake tare sojin, sun kuma kwaci motoci da bama-bamai

Asali: Twitter
Kokarin Sojin Najeriya na su kwaso abokan aikinsu dake daji har suna rubewa yaci tura, bayan da suka sake arangama da mayakan Boko Haram dake kewayen dake wurin, kuma aka sake dauki ba dadi dasu, har ma sun sake karkashe su da ma kwasar makamai, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Alamu dai na nuna bayan wancan harin na Metele a Guzumala LGA, a makon jiya, mayakan Boko Haram ba tserewa suka yi ba, zamansu suka yi a yankin, kuma sun hana a shiga ko a fita daga garin.
Bataliya ta 119 ce dake Bagam inda sojojin suka hallara, taje domin ta kwaso gawarwakin na bataliya ta 157, amma sai aka sami asarar rayuka da manyan makamai.
DUBA WANNAN: Gwamnati zata baiwa FRSC makamai
Majiyarmu, tace, "a safiyar jiya misalin 10:00am sun mana kwanton bauna, sun kuma sake kame mana mutane, sun kuma kwace motocin yaki na igwa da manyan bindigogi, amma munyi nasarar kwaso gawarwaki shuda daga wadanda muka je debowa"
A shekaru kusan goma da ake wannan yaki dai, an sha korar Boko Haram daji, amma sai su dawo.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng