Boko Haram: Faifan bidiyon korafin rashin kayan aiki da sojoji suka saki
Wasu sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram sun saki faifan bidiyo suna zargin cewa rashin ingantatun makamai da basu dashi ya janyo mutuwar 'yan uwansu da dama a harin da aka kai a sansanin soji da ke Metele a Borno.
Sun ce duk da irin dimbin kudaden da ake cewa ana kashewa wajen yaki da Boko Haram, su har yanzu ba samar musu da sabbin makamai na zamani ba an bar su suna fama da tsoffin bindigu da motocin yaki da ke bukatar gyara.
A cikin bidiyon mai tsawon mintuna 5 da AFP ta gani a ranar Asabar, wani soja yana nuna motocinyaki da wasu makamai da mayakan na Boko Haram suka lalata a sansanin na Metele a yayin harin da suka kai a ranar 18 ga watan Nuwamba.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Harin Metele: Adadin sojojin da aka kashe ya karu
Fitowar wannan bidiyon ya yi karin haske kan korafe-korafen da wasu jami'an soji da aka aike da su yankin arewa maso gabas da ke kusa da tafkin Chadi inda suka ce sun dade suna yaki da Boko Haram amma ba basu wani hutu ba.
"Sama da sojoji 100 sun mutu a nan, wasu da dama har yanzu bamu gansu ba," inji sojan da ke magana a cikin faifan bidiyon wadda majiyar Legit.ng ta samu daga majiyar soji da ya tabbatar da sahihancin ta.
"Duba irin makaman da suka bamu a nan. Mafi yawancinsu ba su aiki," inji sojin yayin da ya ke nuna wasu motocin yaki da makamai da suka kone.
"Wadannan duk tsaffin makamai ne da sun dena aiki. Sun ajiye su ne kawai saboda ganin ido.
"Kashe mu kawai akeyi a kullum, lamarin yana kara tabarbarewa," inji shi.
Har yanzu dai hukumar sojin Najeriya ba ta ce komai a kan bidiyon ba.
Anyi hasashen cewa sama da mutane 27,000 ne suka rasa rayyukansu a shekaru tara da akayi ana fama da masifar 'yan ta'addan Boko Haram kuma misalin mutane miliyan 1.8 ne suka rasa muhallinsu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng