Hukumar Soji ta saki tubabbun 'yan Boko Haram 155 a jihar Gombe

Hukumar Soji ta saki tubabbun 'yan Boko Haram 155 a jihar Gombe

Hukumar Sojin Najeriya ta sanar da cewa ta saki tubabun mayakan kungiyar Boko Haram 155 bayan sun kwashe watanni 11 karkashin shirin 'Operation Safe Corridor' na sauya musu tunani da koyar da su sana'o'i domin su zama 'yan kasa nagari.

Shugaban shirin Operation Safe Corridor, Manjo Janar Bamidele Shafa ne ya bayar da sanarwar a yau Asabar a bikin yaye tubabun 'yan ta'addan a wani sansanin bayar da horo da ke jihar Gombe.

Ya ce za a mayar da tubabin 'yan ta'adan garuruwansu bayan an bayan an koyar da su sana'o'i kuma an sauya musu mugan tunaninsu.

Hukumar Soji ta saki tubabun 'yan Boko Haram 155 a jihar Gombe
Hukumar Soji ta saki tubabun 'yan Boko Haram 155 a jihar Gombe
Asali: Twitter

Shafa ya bayyana cewa wannan shine karo na biyo da hukumar sojin ke sakin tubabun mayakan Boko Haram da aka yaye a karkashin shirin na sauya tunaninsu da koyar da su sana'o'i da aka fara tun shekarar 2016.

DUBA WANNAN: An gano wata makabarta da ake binne layu a Kano

Shugaban shirin ya yi kira da sauran mayakan Boko Haram da ke cikin daji da su fito su ajiye makamansu su mika wuya ga Hukumar Sojin Najeriya domin su ma a basu horon sauya tunanin sannan su koma garuruwansu.

Manjo Janar Shafa ya kara da cewa hukumar sojin tana saka idanu a kan tubabun mayakan ta hanyar amfani da masu sarautun gargajiya da 'yan agajin sa kai 'Civilian JTF' da wasu hanyoyin tattaro bayannan sirri bayan an sake su.

Shugaban hedkwatan tsaro, Janar Ayobami Olanishakin ya ce an yaye tubabun mayakan Boko Haram 254 tun fara shirin na Operation Safe Corridor a shekarar 2016 kuma duk sun koma gida suna rayuwa da iyalensu a yanzu.

Da ya ke magana a madadin tubabun 'yan Boko Haram din, Abba Shuwa ya yi kira ga al'umma su yafe musu abinda su kayi a baya inda ya ce a halin yanzu tunaninsu ya canja kuma su 'yan kasa nagari ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164