Kisan sifeto: 'Yan sanda sun kama 'yan Biafra 34 a Nnewi
Hukumar 'yan sandan Najeriya ta kama 'yan kungiyar tayar da kayar baya ta IPOB bisa kisan wani dan sanda mukamin sifeto tare da raunata DPO da wasu ragowar jami'an 'yan sanda a wani artabu da su ka yi jiya a garin Nnewi dake jihar Anambra.
SP Haruna Mohammed, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Anambra, ne ya bayyana hakan a yau, Asabar.
Ya kara da cewar an aika rundunar 'yan sanda mai yawa zuwa garin na Nnewi domin tabbatar da cewar ba a kara samun barkewar wani rikici ko samun tashin hankali ba.
A jiya ne jaridar Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar 'yan sanda biyu da mambobin kungiyar Biyafra sun mutu yayin wata arangama a yau, Juma'a, a garin Nnewi dake jihar Anambra.

Asali: Twitter
Sai dai hukumar 'yan sanda a jihar ta Anambra sun ce dan sanda daya ne ya mutu yayin da DPO din ofishin yankin ke kwance a asibiti bayan ya samu raunuka yayin artabun.
DUBA WANNAN: Tone-tone: Jonathan ya bayyana gwamnonin da su ka ci amanarsa a 2015
Da yake magana da majiyar mu ta wayar tarho, Mike Okoli, mataimakin kwamishinan 'yan sanda mai kula da aiyuka a jihar Anambra, ya ce, "zan iya baku tabbacin cewar mun yi rashin jami'in dan sanda guda mai mukamin sufeto. Sannan DPO din da su ke tare ya samu raunuka, kuma yanzu haka yana asibiti. Wannnan shine abinda na sani."
Rahotanni sun bayyana cewar 'yan kungiyar ta Biyafra sun kewaye garin Nnewi domin gudanar da zanga-zangar neman a gudanar da zaben raba gardama da zai ba su damar kafa kasar Biyafra ta 'yan kabilar Igbo.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng