Kisan sojoji: Shugaba Buhari ya kira shugabanin soji taron gaggawa

Kisan sojoji: Shugaba Buhari ya kira shugabanin soji taron gaggawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya kra shugabanin hukumomin sojojin Najeriya zuwa wata taron gagawa sakamakon rahoton kashe wasu sojojin Najerya da mayakan Boko Haram su kayi a ranar Lahadi a garin Metele da ke iyakan Najeriya da Chadi.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta gano cewa an kiran taron ya zama dole ne saboda kallubalen tsaro da ake fama da shi a Arewa maso gabashin na kasar.

Wani kwakwaran majiya da ya nemi a sakayya sunansa ne ya tabbatarwa NAN kiran taron a Abuja.

Kisan sojoji: Shugaba Buhari ya kira shugabanin soji taron gaggawa
Kisan sojoji: Shugaba Buhari ya kira shugabanin soji taron gaggawa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An gano wata makabarta da ake binne layu a Kano

Majiyar Legit.ng ta gano cewar gwamnatin tarayya ta jinkirta bayyana sunayen sojojin da suka rasu sakamakon harin da Boko Haram ta kai ne saboda ana tuntubar iyalensu.

"Shugaban kasa ya kira taron gagawa da shugabanin hukumomin tsaro.

"Kuma gwamnati tana tuntubar iyalan sojojin da suka rasu kafin tayi tsokaci kan mumman harin da ya afku.

"Wannan shine dalilin da yasa har yanzu gwamnati ba ta ce komai a kan harin ba," inji majiyar.

A baya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura ministan tsaro, Birgediya janar Mansur Dan-Ali (mai ritaya), zuwa kasar Chadi domin halartar wani taro na gaggawa da shugaban kasar, Idris Deby, a kan tabarbarewar tsaro a yankin Najeriya da ya yi iyaka da kasar Chadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164