Bidiyo: Ya dawo gida ya taras da matarsa a gado, tare da wanda bayyi tsammani ba
- Wani mutum ya kama matarshi tare da wani
- Mijin bai aikata komai a garesu ba
- An yada wannan bidiyo a kafafen sadarwa na zamani

Asali: Instagram
Wani mutum ya kama matarshi a gado daya tare da wani dalibi a kasar Zambia.
Mutane da dama sunyi tunanin zai rufesu da duka amma kuma abun mamaki sai bai aikata hakan ba.
An yada wannan bidiyo a kafafen sadarwa na zamani inda dalibin yake kuka shi kuma mijin matar yanayi masa tambayoyi cikin nutsuwa.
DUBA WANNAN: An sako kamsilolin da aka sace a Katsina
A daya bangaren kuma matar ta kauda fuskar ta gefe sannan ta boye fuskar ta saboda kunya ba tare da ta data furta komai ba.
Duba da yanda mijin matar yake karfaffa anyi tunanin zaiyi dukan kawo wuka amma sai baiyi ba.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng